Ko anini ba zan ba da ba: Shehu Sani ya ce ba dashi ba biyan deliget a zaben fidda gwani

Ko anini ba zan ba da ba: Shehu Sani ya ce ba dashi ba biyan deliget a zaben fidda gwani

  • 'Yan takarar gwamnan jihar Kaduna na ci gaba da shiri, wasu kuma na ajiye burinsu na gaje gwamna El-Rufai
  • A wani rahoton da muka samo, Datti Ahmed ya hakura da takara, Shehu Sani kuwa ya yi karin haske kan lamarin
  • Shehu Sani ya bayyana cewa, shi ba zai ba kowane deliget kudi da sunan ya zabe shi ba yayin da ake ci gaba da zaben fidda gwani

Kaduna - Tsohon dan majalisa daga jihar Kaduna, Datti Ahmed, a ranar Talata ya bayyana janyewarsa daga takarar gwamnan jihar Kaduna.

Bayan haka kuma, wani dan takaran, Shehu Sani, ya ce yana ci gaba da fafutukarsa ta fitowa takarar gwamna a jam’iyyar PDP.

Batun Shehu Sani kan ba deliget kudi
Ko anini ba zan ba ku ba: Shehu Sani ya ce ba dashi ba biyan deliget a zaben fidda gwani | Hoto: Olubiyo Samuel
Asali: Original

Sani, wanda tsohon Sanata ne, ya kuma sha alwashin cewa ba zai baiwa deliget cin hancin da za su zabe shi ba.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Ɗan takarar gwamna a PDP ya janye daga zaɓen fidda gwani, ya fara shirin komawa APC

A cewar Shehu Sani a shafinsa na Twitter:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kada wanda ya kuskura ya biya kowane deliget a madadina.
“Ban yi imani da tsarin siyasa na biyan kudi don a zabe ni ba. Wannan bai dace da akida ta da dabi'a ta ba.
“Ina maraba da kuri’un deliget-deliget da za su zabe ni bisa ka’idojin da na tsaya a kai da kuma ajandar da zan yi wa mutanen Jihar Kaduna nagari.
“Ba za mu iya ginawa da bunkasa kasarmu da ‘yantar da jama’armu daga kangin bauta ba ta hanyar gurbataccen tsari na siyasa da muka rungumar babakkere ba.
“Ya kamata jam’iyyar adawa ta zama abin dogaro kuma abin koyi ga gaskiya, adalci da daidaito.
“Wadanda suke tsammanin ko kuma suke kirana na basu miliyoyin domin su zabe ni kada su bata lokacinsu. Kuma ku yi watsi da duk wani daga cikin kodinetoci na da za su yi kokarin yin alkawuran karya kan matsayina.

Kara karanta wannan

Daga korafi a Facebook: Mutumin da gwamnan APC ya daure saboda sukar gwamnatinsa ya kubuta

"Na yi imani ko dai a yi nasara ko kuma a yi rashin nasara da mutunci."

Shehu Sani: Dan takarar PDP ya kwato N100m daga hannun deleget ta hanyar amfani da mafarauta da ’yan banga

A wani labarin, wani dan takarar kujerar majalisar tarayya a jihar Kaduna ya yi nasarar kwato kimanin naira miliyan 100 da ya baiwa deleget din jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin toshiyar baki gabannin zaben fidda dan takarar jam’iyyar.

Tsohon sanata da ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta takwas, Shehu Sani ne ya bayyana hakan a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a yammacin ranar Talata, 24 ga watan Mayu.

Sani ya bayyana cewa dan takarar ya kwato kudin ne bayan ya gaza samun tikitin jam’iyyar a zaben fidda gwanin da aka yi, kuma ya yi amfani da 'yan banga da mafarauta ne wajen karbo kudin nasa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jami'an EFCC sun tasa keyar sanata Okorocha daga gidansa

Asali: Legit.ng

Online view pixel