Yanzu-Yanzu: Sanata da wasu yan takara 6 sun janye daga zaben fidda gwanin PDP, jerin sunayen su

Yanzu-Yanzu: Sanata da wasu yan takara 6 sun janye daga zaben fidda gwanin PDP, jerin sunayen su

  • Sanata Abaribe da wasu yan takarar gwamna Shida a PDP sun janye daga zaɓen fidda gwani na jihar Abia
  • Yan takarar guda 7 sun sanar da matakin janyewar ne bayan wani taron gaggawa da suka yi a gidan tsohon sakataren gwamnatin Abia
  • A halin yanzun sun bar mutum biyu kacal su fafata a zaɓen fitar da ɗan takara ɗaya tilo da zai kare martabar PDP a babban zaɓen gwamna 2023

Abia - Shugaban marasa rinjaye na majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya janye daga fafatawa daga zaɓen fidda gwani na zaɓen gwamnan Abia, awanni kaɗan kafin farawa.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Sanata Abaribe ya fitar ranar Talata.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Bayan fara zaɓen fidda gwani, Tsohon Minista ya janye daga takara karkashin PDP

Yan takara Bakwai sun janye a Abia.
Da Duminsa: Sanata Abaribe da wasu yan takarar gwamna 6 sun janye daga zaɓen fidda gwanin PDP a Abia Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Sanarwan ta ce:

"Ni, Sanata Enyinnaya Harcourt Abaribe, ba zan shiga zaɓen ba saboda haka na janye daga takara, wanda hakan na nufin ba zan fafata a zaben fitar da ɗan takarar gwamnan Abia ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Saboda haka ina kira ga mutanen mu, dumbin magoya baya da su kwantar da hankalin su, su jira mu zamu sanar da mataki na gaba ba da jimawa ba."

Wasu yan takara shida sun bi sahun Sanatan

Bayan sanata Abaribe, wasu yan takara Shida sun janye daga shiga zaɓen fitar gwanin PDP na jihar Abia a hukumance.

Yan takarar da suka janye sun haɗa da mataimakin gwamna, Ude Oko Chukwu, Sanata Emma Nwaka, Nana Nwafor, Dakta Sampson Orji ( Scourj), Chima Anyaso, da kuma Ncheta Omerekpe.

Sun sanar da matakin janyewa ne bayan wani taron gaggawa da suka gudanar a gidan tsohon sakataren gwamnatin jihar, Eme Okoro, da ke Umuahia, babban birnin Abia.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Tashin hankali yayin da PDP ta dage zaben fidda gwani bayan barkewar rikici

Dukkanin yan takarar kujera lamba ɗaya a jihar sun halarci taron amma ban da mutum ɗaya wato Mista Omerekpe, kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.

Bisa samun wannan cigaban, a halin yanzu an bar mutum biyu a tseren takarar tikitin gwamnan, su ne Farfesa Isaac Ikonne, da kuma Mayor Lucky Igbokwe (Don Lulu).

A wani labarin kuma Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kwankwaso da wasu biyu sun fice daga NNPP, sun koma APC a Kano

Yayin da kowace jam'iyya ke shirin tunkarar zaɓen 2023, siyasar Kano na ɗaya daga cikin wacce ta fi jan hankali a Najeriya.

Wasu mambobin majalisar jihar Kano da suka haɗa da mai wakiltar mazaɓar Kwankwaso wato Madobi sun fice daga NNPP sun koma APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel