Wanda ya fara lale N100m ya saye fam a APC ya bayyana inda ya samu kudin shiga takara

Wanda ya fara lale N100m ya saye fam a APC ya bayyana inda ya samu kudin shiga takara

  • Chukwuemeka Nwajiuba ya ce talakawa su ka ba shi gudumuwar tsayawa takara a zaben 2023
  • Tsohon karamin Ministan ilmin shi ne ya fara sayen fam din neman zama shugaban kasa a APC
  • Mutane 3100 su ka ba Hon. Chukwuemeka Nwajiuba gudumuwa, a ciki har da wani manomin doya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Emeka Chukwuemeka Nwajiuba, daya daga cikin masu neman takarar kujerar shugaban kasa a APC, ya bayyana yadda ya samu kudin sayen fam.

A ranar Talata, 24 ga watan Mayu 2022, NNN ta rahoto Chukwuemeka Nwajiuba yana fadawa ‘yan jarida cewa talakawa suka taimaka masa da gudumuwa.

Da yake zantawa da manema labaran a garin Abuja, tsohon Ministan ilmin ya ce ba manya su ka turo shi takara ba, amma ya yarda kudi ya bata harkar siyasa.

Kara karanta wannan

Rade-radin takara a APC na kara karfi, Goodluck Jonathan ya yi kus-kus da Mamman Daura

The Cable ta rahoto cewa Hon. Nwajiuba ya yi ikirarin sama da mutum 3000 suka hada masa kudi domin ya mallaki fam din tsayawa takara a APC mai mulki.

A cewar tsohon ‘dan majalisar, akwai wani Bawan Allah wanda ya bada gudumuwar doya da nufin a saida, a samu kudin da zai nemi kujerar shugaban kasa.

‘Dan siyasar ya tabbatar da cewa kan masu neman takara a APC daga kudu maso gabas bai hadu ba duk da zaman da aka yi domin marawa mutum daya baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Chukwuemeka Nwajiuba
Hon. Chukwuemeka Nwajiuba Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Abin da Emeka Chukwuemeka Nwajiuba ya fada

“Dole in yarda da ku cewa mun maida siyasa ta kudi, amma ina mai tabbatar maku da mun samu Muhammadu Buhari wanda ya zama shugaban kasa kuma bai da kudi.”
“Na gabatar da kai na ne kurum domin yi wa al’umma hidima. Ba kamfanonin mai ke daukar dawainiyar takarata ba, saboda haka ‘yan Najeriya ne ke taimaka mani.”

Kara karanta wannan

Abin da ya sa ba zan ba masu tsaida takara a PDP ko sisi ba - Mai neman Gwamnan Kano

“Mutane 3, 150 suka bada gudumuwa, sannan mu ka saye wadannan fam na shiga takara.”
“Ina da wadanda suka je majalisar wakilan tarayya tun a shekarar 1992 da suka mara mani bayan fitowa neman shugaban kasa, tun kafin a fara tattara mani gudumuwa."
“Wasu sun bada N1, 000, akwai wani mutumi daga Nasarawa da ya bani doya 150 in saida. Mutane su na sa kudinsu a tafiyar ne da nufin ganin Najeriya tayi kyau nan gaba.”

- Emeka Chukwuemeka Nwajiuba,

Kamar yadda labari ya zo daga NAN, Nwajiuba ya yi alkawari zai yi biyayya idan shugabannin jam’iyyar suka fito da ‘dan takarar 2023 ta hanyar yin maslaha.

'Yan takarar karya a APC

Ku na da labari Kayode Fayemi ya ziyarci jihar Neja da nufin samun kuri’un ‘ya 'ya yan APC a zaben fitar da gwani, inda ya caccaki wasu abokan hamayyarsa.

Dr. Fayemi ya zargi wasu ‘yan takarar da cewa sun cika wuri ne kurum, amma ba da gaske suke yi ba. A cewarsa masu takara da gaske ba su wuce mutane biyar ba.

Kara karanta wannan

Zulum: Allah ke ba da mulki, ba zan roki wani ya dauke ni abokin takarar shugaban kasa ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng