Gwabzawar 2023: Fintiri ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan PDP a Adamawa

Gwabzawar 2023: Fintiri ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan PDP a Adamawa

  • Gwamna mai ci, Ahmadu Finitiri ya sake samun damar sake yin takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP
  • Gwamnan, wanda ya sanar da sake fitowarsa takara a watan Afrilu ya shaida cewa, yana shirye ne don ci gaba da aiki daga inda ya tsaya
  • A yau ne aka yi zaben fidda gwani, kuma jam'iyyar ta sake bashi tikitin takara na zaben 2023 mai zuwa nan kusa

Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP a jihar.

Channels Tv ta ruwaito cewa, gwamnan jihar ya yi nasara da jimillar kuri’u 663 daga cikin 668 da kuri’u 5 daga cikin kuri’un da aka kada.

Finitiri ya lashe zaben fidda gwani na PDP
Da dumi-dumi: Fintiri ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan PDP na Adamawa | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamnan, wanda ya sanar da sake tsayawa takara a watan Afrilu, ya ce zai ci gaba da kokarin raya jiha kamar yadda gwamnatinsa ta tsara.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bayan janyewa daga takarar shugaban kasa, Peter Obi ya fice daga PDP

TheCable ta rahoto Fintiri na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mun yi abubuwa da yawa kuma akwai sauran abubuwan da za a yi don kyautata dimbin jama’armu da jiharmu abar kaunarmu. Mun kulla alakar amana da masu zabe, wadanda akasarinsu talakawa ne inda muke samun goyon baya domin jam’iyyar mu na bukatar ci gaba a kan turbar nasara.
“Bayan tattaunawa mai zurfi a cikin babbar jam’iyyarmu da wajenta, a cikin jihar da wajenta, da ‘yan uwana, abokaina da shugabanni, ina so in sanar da ku cewa na amince na sake mika kaina don neman goyon bayan jam’iyyar. goyon bayan babbar jam'iyyar mu ta PDP na dauki tutarta a zaben gwamna na 2023."

Shirin 2023: Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara ya janye daga takarar gwamna a PDP

A wani labarin, gabanin zaben fidda gwani na gwamna na jam'iyyar PDP, tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara Barista Mahdi Aliyu Gusau ya fice daga takarar.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Tashin hankali yayin da PDP ta dage zaben fidda gwani bayan barkewar rikici

Channels Tv ta rahoto cewa, Mahdi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakatarensa Umar Aminu a Gusau babban birnin jihar Zamfara ranar Laraba.

Mahdi Gusau ya bukaci deliget-deliget, shugabannin jam’iyyar, da magoya bayansa da su zabi Dr. Lawal Dauda ya zama dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar ta Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel