Rade-radin takara a APC na kara karfi, Goodluck Jonathan ya yi kus-kus da Mamman Daura

Rade-radin takara a APC na kara karfi, Goodluck Jonathan ya yi kus-kus da Mamman Daura

  • Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi zama da Malam Mamman Daura a gidansa jiya
  • Ana tunanin makasudin zaman bai wuce burin wasu na ganin Goodluck Jonathan ya karbi mulki ba
  • Rade-radi na kara yawo cewa Dr. Jonathan yana shirin tsayawa takarar shugabancin kasa a APC
  • Ana zargin Mamman Daura yana cikin masu motsa gwamnati, ‘danuwa ne ga Muhammadu Buhari

Abuja - Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya yi zama da Malam Mamman Daura wanda ‘danuwa ne wajen Muhammadu Buhari.

Rahoton da ya fito daga jaridar Punch a ranar Laraba, 25 ga watan Mayu 2022, ya tabbatar da cewa Dr. Goodluck Jonathan ya sa labule da Mamman Daura

Ana zargin Jonathan ya hadu da Mamman Daura a gidansa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Mun gano take-taken, Goodluck Jonathan ne 'Dan takarar Buhari a zaben 2023 inji Kungiyar APC

Wani hoto da Sahara Reporters ta fitar ya nuna tsohon shugaban na Najeriya yana gaisawa da dattijon da ake gani ya na da ta-cewa a gwamnati mai-ci.

A hoton za a ga wani mutumi a baya yayin da manyan suke gaisawa. Ba mu iya gane wanane shi ba, amma daga irin shigarsa, da alamar cewa Bahaushe ne.

Masu fashin bakin siyasa su na ganin Jonathan ya hadu da Daura ne a shirye-shiryen da ake yi na ganin an tsaida shi takarar shugaban kasa a APC a 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Goodluck Jonathan da Mamman Daura
Jonathan na gaisawa da Mamman Daura Hoto: saharareporters.com
Asali: UGC

Za a fara tantance masu takara

Nan da gobe ake sa ran APC za ta soma tantance masu neman tsayawa takarar shugaban kasa, kuma Jonathan yana cikin wadanda aka sayawa fam din.

Legit.ng Hausa ta fahimci Goodluck Jonathan yana cikin wadanda aka cike fam dinsu, ko da farko ya nuna bai amince da karambanin da aka yi masa ba.

Kara karanta wannan

Mai neman takara ya samu tikitin PDP yayin da yake hannun masu garkuwa da mutane

Za a kara gaskata maganar ganin tsohon shugaban na Najeriya ya hadu da shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu cikin wani dare a watan nan.

Mamman Daura a gwamnatin Buhari

Kwanakin baya Malam Daura ya dauki tsawon lokaci yana kasar Ingila, sai daga baya ya dawo Najeriya. Ana zargin yana zama ne a fadar shugaban kasa.

Mamman Daura tamkar ‘da yake a wajen shugaban Najeriya, duk da cewa ya girmi Mai girma Muhamamadu Buhari da shekaru uku da wasu 'yan kwanaki.

An dade ana rade-radin dattijon yana cikin masu juya akalar gwamnatin Buhari, zargin da shugaban kasar ya dade da musanyawa da aka yi hira da shi.

Take-taken da ake yi a APC - Kungiya

Dazu aka samu labari cewa wata kungiya da ke cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fito ta na cewa akwai yiwuwar a ba Goodluck Jonathan takara.

Wannan kungiya ta The APC Watchdog ta fitar da jawabi na musamman a game da shirin dawo da Dr. Jonathan kan kujerar da ya rasa a zaben da aka yi a 2015.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya bayyana irin yadda yake matukar son gaje Buhari, ya ce ba wasa yake ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel