Rikicin gidan PDP ya jagwalgwale a Kano, an rasa gane wadanda za su yi takara a 2023

Rikicin gidan PDP ya jagwalgwale a Kano, an rasa gane wadanda za su yi takara a 2023

  • Har yanzu an gagara fahimtar su wanene za su yi wa PDP takarar kujerun majalisa a jihar Kano
  • Bangarorin Shehu Sagagi da na Bello Gwarzo sun gudanar da mabambantan zaben tsaida gwani
  • Kowane bangare yana ikirarin shi yake da iko da jam’iyyar hamayyar, yanzu magana ta na kotu

Kano - Ana cikin wata kwamacala a jam’iyyar PDP ta reshen jihar Kano domin bangarori biyu su ka gudanar da zaben tsaida gwani na shiga takarar 2023.

Rahoton da Daily Trust na yammacin Talata, 24 ga watan Mayu 2022, ya ce tsagin Shehu Wada Sagagi da na Bello Hayatu Gwarzo duk sun shirya zabe.

Wadannan bangarorin PDP biyu da ke rigima a kotu sun gudanar da zaben tsaida gwani na ‘yan takarar majalisar dokoki, majalisar tarayya da na Sanatoci.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Gwamnonin APC sun shirya tsaf domin zaban dan takarar da zai gaji Buhari

Wannan lamari ya jefa masu harin takara a karkashin jam’iyyar da mabiyansu a cikin rashin tabbas.

An yi zabe kashi-kashi

A yammacin ranar Lahadi, ‘yan bangaren Bello Hayatu Gwarzo su ka shirya zabukan tsaida ‘yan majalisa a kananan hukumomi 44 da ake da su a jihar Kano.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Washegari watau Litinin ne tsagin Shehu Wada Sagagi suka gudanar da na su zaben fitar da gwanin. Duka bangarorin ba su fitar da na su sakamakon ba.

Manyan PDP na Kano
Amb. Aminu Wali da Sanata Bello Hayatu Gwarzo Hoto: @FreedomRadioNigeria
Asali: Facebook

Wata majiya daga ofishin INEC na jihar Kano ta shaidawa jaridar cewa ta sa ido wajen gudanar da zaben, amma ba a san na wani bangare aka yarda da shi ba.

Amma Hukumar INEC ta ce ba a kawo mata sakamakon zaben da aka gudanar domin a tattara ba.

Rahoton ya ce har zuwa yanzu ana tattara kuri’un da ‘ya ‘yan jam’iyyar hamayyar suka kada ne. Da zarar an gama wannan, za a sanar da wadanda suka yi nasara.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar dattawa: Ni na ke da duk abin da ya dace na gaje kujerar Buhari

'Ya 'yan PDP su na magana biyu

Legit.ng Hausa ta fahimci mabanbantan hotunan sakamakon zabe su na yawo. Misali an rasa gane wanda zai yi wa PDP takara a yankin Kano ta tsakiya a 2023.

Wasu bangaren su na cewa Hon. Abubakar Nuhu Danburam ne ya lashe zaben tsaida gwani. A gefe guda kuma akwai masu ikirarin Laila Buhari ce ta yi nasara,

Kotu ta ba Sagagi gaskiya

Jiya aka ji labari wata kotu da ke zama a Kano ta jaddada cewa Shehu Wada Sagagi ne shugaban jam'iyyar PDP na reshen jihar, akasin hikuncin da aka yi kwanaki.

Ana zargin Sagagi na hannun dama ne ga tsohon gwamnan Kano kuma dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar NNPP, don haka ake neman tunbuke shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel