Zaben fidda gwanin PDP: DPO ya sha ruwan duwatse, an kashe wani a Gombe

Zaben fidda gwanin PDP: DPO ya sha ruwan duwatse, an kashe wani a Gombe

  • An samu tashin hankali a yayin zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP da aka yi a ranar Lahadi a karamar hukumar Billiri ta jihar Gombe
  • Lamarin ya yi sanadiyar rasa ran wani yayin da aka yiwa shugaban yan sandan yankin (DPO) ruwan duwatsu har ta kai ga an fasa masa goshi
  • Rigimar ya samo asali ne lokacin da jami'an tsaro suka fatattaki wasu magoya bayan yan siyasa daga wajen zaben

Gombe - Rahotanni sun kawo cewa wani mutum ya rasa ransa a yayin zaben fidda gwani na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ya gudana a karamar hukumar Billiri da ke jihar Gombe, a yammacin ranar Lahadi.

An tattaro cewa lamarin ya afku ne lokacin da jami’an yan sanda da ke wajen zaben suke kokarin korar wasu magoya bayan yan siyasa da ke kokarin kawo hargitsi daga wajen zaben fidda gwanin na PDP a mazabar Billiri/Balanga.

Kara karanta wannan

Rundunar yan sanda ta tabbatar da kisan mutum 12 a wani harin sassafe da yan bindiga suka kai Katsina

Zaben fidda gwanin PDP: DPO ya sha ruwan duwatse, an kashe wani a Gombe
Zaben fidda gwanin PDP: DPO ya sha ruwan duwatse, an kashe wani a Gombe Hoto: Premium Times
Asali: UGC

An gudanar da zaben ne a Tangji, wani yanki da ke wajen garin Billiri inda aka rahoto cewa an fasawa DPO na ofishin yan sandan Billiri da ke saka ido kan ayyukan tsaro a wajen zaben goshi sakamakon ruwan duwatsu da aka yi masa.

Hakan ne ya haddasa bacin rai wanda ya yi sanadiyar harbin wani mai goyon bayan yan siyasar inda wani ya kuma ji mummunan rauni a kafadunsa, Nigerian Tribune ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai kuma, da yake tabbatar da lamarin ga jaridar Thisday a wata hira ta wayar tarho, kwamishinan yan sandan jihar Gombe, Ishola B Babaita, ya nesanta kisan da zaben fidda gwanin.

A cewar kwamishinan yan sandan, kisan bai da kowani alaka da zaben fidda gwanin domin ya faru ne a nesa da waen zaben fidda gwanin yana mai bayar da tabbacin cewa ana kan bincike domin sanin gaskiya abun da ya faru har ya kai ga mutuwar wani.

Kara karanta wannan

2023: INEC ta bayyana mummunar illar da dage zabukan fidda gwani za su a zabe mai zuwa

Ya ce:

“Kisan bai da nasaba da zaben fidda gwanin domin ya wakana ne nesa da wajen zaben.”

Wani ɗan takara a jam'iyyar PDP ya yanke jiki ya faɗi bayan shan kaye da zaɓen fidda gwani

A wani labarin, mun ji cewa dan takarar kujerar majalisar wakilan tarayya karkashin inuwar PDP, Dakta Philip Okwuada, a ranar Litinin, ya yanke jiki ya faɗi sumamme bayan shan kaye a zaɓen fidda gwani a jihar Delta.

Wakilin Punch ya tattaro cewa Mista Okwuada, wanda ya shiga neman tikitin takarar ɗan majalisa mai wakiltar Ika a majalisar dokokin tarayya, ya faɗi ne yayin da yake hira da yan jarida jim kaɗan bayan sanar da sakamako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel