Kamfanin wutar lantarkin Najeriya
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa 'yan Najeriya sun kashe kudaden da suka kai N16tr wajen siyan janaretoci da man fetur domin samun lantarki a 2023.
An sake yin karin kudin wutar lantarki ga 'yan tsarin 'band A' da ke ƙarƙashin ikon kamfanin rarraba wutar na Kaduna (KAEDCO) daga N206.80/kWh zuwa N209.5/kWh.
Gwamnatin tarayya da rundunar 'yan sanda sun ce babu wani abin fashewa da ya tashi a tashar wutar lantarki ta Zungeru ranar Litinin. An ce rahoton karya ne kawai.
Hukumar jami'ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil sun shiga tsilla-tsilla bayan kamfanin rarraba hasken wuta, KEDCO ya yanke masu wuta.
An zargi jami'an rundunar sojojin saman Najeriya da lakadawa ma'aikatan kamfanonin wutar lantarki dukan tsiya a Legas. Sun yi hakan ne bayan an datse musu wuta.
Jihohi biyu na Kudu maso Yamma za su fuskanci daukewar wutar lantarki yayin da kamfanin rarraba wutar lantarkin Najeriya ya bayyana shirin gudanar da muhimmin gyara.
Gwamnatin jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da dakatar da dagaci da kansila a karamar hukumar Akko bisa zargin sace randar wutar lantarki
Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki (KEDCO) ta maka kungiyar masu sarrafa kayan abinci na kasa (MAN) gaban kotun babbar tarayya da ke Abuja saboda jawo asara.
Wasu fusatattun mata daga yankin Ipo a Ribas sun shiga zanga-zanga domin nunawa mahukunta bacin ransu na rashin wuta da su ke fama da shi a yankunansu.
Kamfanin wutar lantarkin Najeriya
Samu kari