Karin Kudin Lantarki: Sanatan APC Ya Soki Gwamnatin Bola Tiunbu

Karin Kudin Lantarki: Sanatan APC Ya Soki Gwamnatin Bola Tiunbu

  • Sanata Ali Ndume ya soki matakin gwamnatin Bola Tinubu na yin ƙatin kuɗin wutar lantarki ga ƴan Najeriya
  • Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu ya bayyana cewa ko kaɗan babu adalci a cikin ƙarin kuɗin lantarkin
  • Ya yi nuni da cewa a halin da ake ciki na tsadar rayuwa a ƙasar nan, bai kamata a ƙara ɗora wani nauyi kan al'ummar ƙasar nan ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sanata Mohammed Ali Ndume, ya koka kan ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi a baya-bayan nan.

Ya soki lokacin yin ƙarin yana mai cewa ƴan Najeriya har yanzu suna cikin shan wahalar cire tallafin man fetur, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya fadi kokarin da zai yi a samu tsaro a jihar Zamfara

Ndume ya caccaki Tinubu
Ali Ndume ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Ali Ndume
Asali: Facebook

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Ndume ya yi Allah-wadai da matakin, ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta sake duba halin da ƴan Najeriya ke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ndume ya kuma soki rashin tuntubar majalisar tarayya wajen ɗaukar wannan matakin.

A kalamansa:

"Akwai kuskure a lokacin da aka yi ƙarin. Ƴan Najeriya na fuskantar ƙalubale masu yawa. Ƙara ɗora musu wannan nauyin ba adalci ba ne.
"Har yanzu ƴan Najeriya ba su gama farfaɗowa daga cire tallafin man fetur a shekarar da ta gabata ba. Ƴan Najeriya da dama na ji a jikinsu kan hakan. Kuskure ne yanzu a zo da wannan ƙarin a wannan lokacin.
"Hauhawar farashin kayayyaki ya yi sama sosai. Farashin abinci, magunguna, sufuri da kuɗaɗen makaranta ya yi tashin gwauron zabi. Ba adalci ba ne a ƙara wani nauyi a wannan lokacin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 19 a wani sabon hari a jihar Arewa

"Ba a ƙara mafi ƙarancin albashi ba. Jihohi da dama ba su biyan mafi ƙarancin albashi na N30,000. Ta yaya a ake son mutane su rayu a haka?"

Ya bayyana cewa kamata ya yi gwamnati ta fara samar da wadatacciyar wutar lantarki, sauko da farashin kayayyaki, dawo da darajar Naira kafin ta ɗauki wannan matakin.

Atiku ya soki ƙarin kuɗin lantarki

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya yi tir da yadda gwamnatin Najeriya ta tashi kuɗin lantarki.

Babban jagoran adawan bai goyon bayan ƙarin kuɗin wutar lantarkin da aka yi wa ƴan rukunin farko da ake kira Band A ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel