Jihar Osun
A labarin nan za a ji cewa yan takarar gwamna a PDP da APM sun kara wa Ademola Adeleke karfi inda suka hakura da neman kujerar gwamnan jihar na gobe.
Gwamnatin jihar Edo ta caccaki Davido kan kiran Shugaba Donald Trump ya sanya ido kan zaben Osun, tana mai cewa ya koma dakin waka maimakon siyasa.
APC ta zargi an kashe ɗan ƙanwar Daraktan Yaƙin Neman Zaɓenta a Osun, yayin da jam’iyyar ta buƙaci ’yan sanda su binciki lamarin gabanin zaɓen gwamna.
Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce APC za ta lashe zaben gwamnan Osun ta hanyar tsarin siyasa ba karfin tarayya ba.
Lauya Timothy Tugbiyele ya bukaci Davido ya nemi afuwar Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, kan wallafa sakamakon WAEC da ake zargin nasa ne.
A labarin nan za a ji yadda jam'iyyar hadakar adawa ta ADC ta hango wa kanta matsala da kalubale a lokaci guda a zaben Osun da ake shirin yi a karshen mako.
Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa an shirya makircin kama tsohon gwamna kuma sakataren jam'iyyar na ƙasa, Rauf Aregbesola, dab da zaɓen gwamna ranar Asabar.
Atiku Abubakar ya gargadi hukumar zabe ta INEC da hukumomin tsaro kan amfani da karfin gwamnati wajen karkatar da zaben gwamnan jihar Osun na 2026.
Hukumar INEC ta ƙara ɗan takarar jam'iyyar SDP, Francis Ajala, cikin zaɓen gwamnan Osun bayan hukuncin kotu, inda jam’iyyun da za su fafata suka koma 15.
Jihar Osun
Samu kari