Omoyele Sowore
Majalisa ta ce ba za ta binciki wani babban abun da ya faru lokacin Saraki ba. Sanata Akwashiki ya ce a Majalisa, babu ruwansu da duk abin da aka yi a 2018.
Legit.ng Hausa ta tattaro maku abubuwan da za su faru a Najeriya a bana daga zabukan Gwamnonin Edo da Ondo, da shirin 2023, karin haraji da dai sauransu.
Mun tsakuro jerin wasu hukunci da kotu su ka yi a Najeriya a cikin wannan shekarar da ake bankwana da ita, wanda su ka bada mamaki. Daily Trust ta fara kawo wannan rahoto.
Bayan fitowarsa Sambo Dasuki ya ce babu wani sabani tsakaninsa da Shugaban kasa. Haka zalika Kanal Dasuki ya shaidawa Duniya cewa bay a fama da wata rashin lafiya.
Shugaban Najeriya ya ce an yi ram da Sowore ne a matsayin ‘Dan gwagwarmaya ba ‘Dan Jarida ba. Garba Shehu ya ce Buhari mutum ne mai bin dokar kasa.
Jami’an hukumar tsaron sirri, DSS, ta sako tsohon dan takarar shugaban kasa, kuma fitaccen dan jaridar nan mai mallakin kamfanin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore, sai dai ta hana shi wayoyin salularsa.
Wani Hadimin Sanata O. Omo Agege, E. Ugbarugba ya sha da kyar bayan an yi yunkurin kashe shi a Delta. An harbi Mai ba babban Sanatan na APC shawara ne cikin dare kamar yadda ya shaidawa Manema labarai.
Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Abuja ta sassauta sharuddan belin da ta gindaya ma shugaban kawo juyin juya hali a Najeriya, kuma mawallacin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore.
Jam’iyyar African Action Alliance (AAC) ta dakatar da shugabanta na kasa, Mista Omoyele Sowore daga jam’iyyar. Haka zalika lamarin ya shafi wasu jami’an jam’iyyar na kasa su 28.
Omoyele Sowore
Samu kari