Garba Shehu ya Rika Aiki da ni Wajen Taya Atiku Yakar Obasanjo - 'Dan takaran AAC

Garba Shehu ya Rika Aiki da ni Wajen Taya Atiku Yakar Obasanjo - 'Dan takaran AAC

  • Omoyele Sowore ya maida martani a game da kalaman da Atiku Abubakar ya fada a game da shi
  • Sowore ya ce Garba Shehu ya rika aiko masa da takardu a lokacin Atiku yana rigima da Obasanjo
  • ‘Dan takaran shugaban kasan na jam’iyyar AAC ya ce bai taba fadawa kowa abin da ya wakana ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - ‘Dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta AAC, Omoyele Sowore, ya yi maganar alakarsa da Garba Shehu a lokacin gwamnatin PDP.

Da aka yi hira da Omoyele Sowore a gidan talabijin na Arise TV, ya maida martani ga Alhaji Atiku Abubakar a kan wasu kalamai da ya yi game da shi.

Sowore ya bada labarin yadda Malam Garba Shehu ya rika aiko masa da takardu domin a maidawa Shugaban Najeriya na wancan lokaci martani.

Kara karanta wannan

Babu boye-boye: ‘Dan takaran Shugaban kasa ya Jero Duk Abin da ya Mallaka a Duniya

A hirar da da aka yi da ‘dan takaran, ya ce sa’ilin da Shehu yake a aiki a gwamnatin PDP, ya rika aika masa da takardun da za su yi wa Obasanjo raddi.

“A lokacin da Garba Shehu yake aiki da shi (Atiku Abubakar), a matsayin mai taimaka masa (SA), ya rika tura mani takardu daga bangarensa.
A karon farko nake fadar wannan magana – yana neman yi wa Obasanjo raddi, a lokacin su (Obasanjo da Atiku) na ta fada da junansu.” - Sowore.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Garba Shehu
Shugaban kasa da Malam Garba Shehu Hoto: GarShehu
Asali: Facebook

Sowore ya na da gidan jaridar Sahara Reporters wanda ta rika fitar da bayanai a game da gwamnatin tarayya a lokacin PDP ta na kan karagar mulki.

An yi ta mamakin yadda jaridar ta rika samun wasu takardu da ke fitowa daga gidan gwamnati. Sowore ya jefi Shehu da zargin aiko masa da bayanai.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar: Ban Taba Zama Fiye Da Wata Daya a Dubai Ba

Rikicin Atiku da Obasanjo

Daily Trust ta rahoto cewa alaka tayi tsami tsakanin Olusegun Obasanjo yayin da yake kan mulki, shi kuma Atiku Abubakar a lokacin yana mataimaki.

Wannan rigima ta yi sanadiyyar da mataimakin shugaban kasar ya sauya-sheka daga PDP zuwa ACN. Daga baya su biyun sun sasanta junansu a 2018.

Kafin zamansa Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya yi aiki da Atiku, wanda kwanaki ya caccaki ‘dan takaran na jam’iyyar AAC.

Legit.ng Hausa ta rahoto 'dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben shekarar 2023 yana cewa Omoyele Sowore bai san komai ba game da Najeriya ba.

Hakan ya biyo bayan Sowore ya ce Atiku yana da hannu wajen jawo tabarbarewar wutar lantarki a lokacin da ya rike kujerar iko a gwamnatin Obasanjo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel