Bayan Kwankwaso, Wani Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Yi Zazafan Martani Kan Goyon Bayan Obi Da Obasanjo Ya Yi

Bayan Kwankwaso, Wani Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Yi Zazafan Martani Kan Goyon Bayan Obi Da Obasanjo Ya Yi

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore ya yi martani kan goyon bayan da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi wa Peter Obi
  • Mawallafin na Sahara Reporters ya ce baya bukatar goyon daga mutanen da ya ce suna cikin wadanda suka lalata Najeriya
  • Sowore ya ce shi goyon bayan da ya ke so daga mutanen Najeriya ne wadanda suka yanke shawarar zaben shugabanni da suke so

Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Action Congress, AAC, ya ce gara ya samu goyon bayan yan Najeriya a maimakon 'mutanen da suka lalata kasar'

Mawallafin jaridar ta Sahara Reporters ya bayyana hakan ne a hirar da Arise TV ta yi da shi a ranar Alhamis.

Omoyele Sowore
2023: Bana Bukatar Goyon Baya Daga Wadanda Suka Lalata Najeriya, In Ji Dan Takarar Shugaban Kasa Na AAC. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Duk Karya Ce Ba Za a Gani a Kasa Ba, Tinubu Kan Alkawaran Zaben da Atiku da PDP Suka Daukarwa Yan Najeriya

Da ya martani kan goyon bayan da Obi ke samu, Sowore ya ce yana bukatar 'hadin gwiwa' daga yan Najeriya ne ba goyon bayan tsaffin shugabannin kasar ba.

Sowore ya kara da cewa ba zai taba ziyarar gidajen tsaffin shugabanin kasar ba don rokon su goyi bayansa, The Cable ta rahoto.

Dan takarar na shugaban kasa na AAC ya ce:

"Hadin gwiwa na ke so. Mutane za su iya goyon baya ba tare da bata sunan su ba.
"Amma, matsayi na kan wannan batun shine bana bukatar goyon bayan mutanen da suka lalata Najeriya. Na bayyana hakan karara.
"Ba zan tafi gidan tsohon shugaban kasa wadanda suka lalata kasar nan ba in ce 'don Allah ka goyi baya na don in zama irin ka.'
"Irin goyon bayan da na ke bukata shine daga mutanen da suka yanke shawarar irin shugabannin da suke so. Bai kamata mutanen da suka kusa barin duniya ba, su rika tursasa wa matasa shugabanni."

Kara karanta wannan

Ba dani ba: IBB ya fadi gaskiya kan cewa yana goyon bayan Peter Obi a zaben bana

Asali: Legit.ng

Online view pixel