Yan Najeriya Za Su Roke Ni In Zarce Shekaru 8 Idan Na Zama Shugaban Kasa, In Ji Sowore

Yan Najeriya Za Su Roke Ni In Zarce Shekaru 8 Idan Na Zama Shugaban Kasa, In Ji Sowore

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC a zaben 2023, Omoyele Sowore, ya ce yan Najeriya za su roke shi ya zarce wa'adi 2 idan ya zama shugaban kasa
  • Sowore, yayin hirar da aka yi da shi a Channels TV ya yi alkawarin bawa daliban makarantun gaba da sakandare tallafin N100,000 duk zangon karatu
  • Mawallafin na Sahara Reporters amma ya ce baya ra'ayin zarce shekaru takwas a mulki don haka wa'adi biyu zai yi idan an zabe shi

Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Action Congress, AAC, ya ce yan Najeriya za su roke shi ya zarce wa'adi biyu da doka ta kayyade na mulki idan ya zama shugaban kasa, rahoton The Cable.

Sowore ya yi magana ne a ranar Laraba yayin tattaunawa da aka yi da shi a Channels Television.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shin Atiku Zai Yi Sulhu Da Boko Haram? Ɗan Takarar Na PDP Ya Bayyana Abinda Ke Zuciyarsa

Omoyele Sowore.
Yan Najeriya Za Su Roke Ni In Zarce Shekaru 8 Idan Na Zama Shugaban Kasa, In Ji Sowore. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

ASUU Ya dace a ba wa kudin da aka kashe wurin sauya fasalin naira - Sowore

Da ya ke magana kan sauya fasalin naira, Sowore ya ce kamata ya yi da an yi amfani da kudin wurin biya wa ASUU bukatunsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce idan an zabe shi shugaban kasa zai mayar da hankali kan habbaka darajar naira a maimakon sauya fasalin kudin, rahoton Head Topics.

Zan bawa kowanne dalibin makarantar gaba da sakandare N100,000 duk zangon karatu - Sowore

A bangaren ilimi, Sowore ya ce idan an zabe shi shugaban kasa, gwamnatinsa za ta rika bawa kowanne dalibin jami'a tallafin N100,000 duk zangon karatu.

Wani sashi cikin jawabinsa:

"Na fada; duk dalibin Najeriya wanda ke makarantar gaba da sakandare - akwai dalibai miliyan 1.7 a makarantun gaba da sakandare - za mu rika bada a kalla N100,000 duk zangon karatu daga gwamnatin tarayya. Ba wasa na ke yi ba. Ba zan sa su karbi bashi ba.

Kara karanta wannan

Shugabbanin Kudu Sun Koka Kan Yadda Aka Maida su saniyar Ware Musamman A Faggen Shugabancin

"Yan Najeriya za su rika roko na in cigaba da mulki bayan wa'adi na guda biyu idan na yi aikin da na ke fada maka. Amma bana son yin fiye da wa'adi biyu; ban ra'ayin hakan."

Sowore Ya Kusa Bawa Hammata Iska da Hamza Al-Mustafa da Kashim Shettima a Wurin Taro

A wani rahoton, an yi yar hayaniya a lokacin da yan takarar shugaban kasa suka tafi sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a babban zaben da za a yi a 2023.

Rikici ya kusa ya kaure ne yayin da Kashim Shettima ya zauna a kujerar da aka warewa dan takarar shugaban kasa, alhali shi dan takarar mataimakin shugaban kasa ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel