Ni Na Taimaki Obi, Da Tuni Ya Ci Taliyar Karshe; Dan Jarida Ya Tono Alherin da Ya Yiwa Tsohon Gwamna

Ni Na Taimaki Obi, Da Tuni Ya Ci Taliyar Karshe; Dan Jarida Ya Tono Alherin da Ya Yiwa Tsohon Gwamna

  • Sowore ya musanta wasu rade-radi da ke da alaka dashi da Peter Obi, inda yake bayyana abubuwan da suka faru a sadda ya goyi bayan tsohon gwamnan Anambra
  • Sowore dan gangamin RevolutionNow yayi ikirarin cewa ya kare tafiyar Obi a matsayin dan takarar jam'iyyar Labour a zaben 2023
  • Ya kuma tuna irin taimakon da ya yiwa Obi a baya a lokacin da yake gwamna, inda ya fallasa makarkashiyar da aka yi masa ta hanyar amfani da Sahara Reporters

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

FCT, Abuja - Omoyele Sowore ya bayyana wani muhimmin sirri na tsawon shekaru game da Peter Obi, mai rike da tutar jam'iyyar Labour Party (LP) a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu ya yi ritaya daga siyasa

Yayin da yake musanta cewa ya damu da Obi, Sowore, tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar AAC, ya ce ba shi ne karon farko da zai taimakawa tsohon gwamnan ba.

Na taimaki Obi a rayuwa, inji Sowore
Sowore ya ce ya taimakawa siyasar Obi | Hoto: Mr. Peter Obi, Omoyele Sowore
Asali: Facebook

Sowore ya kuma yi ikirarin cewa shi ne ya taimaka wajen fitowar Obi a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour inda ya kara da cewa shi ne ya bayar da takardar da aka yi amfani da ita don samun gurbi a jam’iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da kadan an tsige Obi a gwamna, Sowore

Dan gangamin na RevolutionNow ya kuma yi nuni da cewa, ya ceci Obi daga barazanar rasa kujerarsa a matsayin gwamna a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Ya kara da cewa ya yi amfani da kafar yada labaransa ta Sahara Reports wajen bankado duk wani makircin da aka kulla wa tsohon gwamnan na jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar dattawa ya yi magana kan rade-radin ya yanke jiki ya fadi a bikin cika shekaru 61

Ya yi magana ne a wani fili tattaunawa mai suna “MIC ON PODCAST” a ranar Asabar, 16 ga Disamba, 2023, in ji jaridar Nigerian Tribune.

Bayani daga Sowore game da Obi

Sowore ya ce:

“Ni ne na ba da takardar da Femi Falana (SAN) ya yi amfani da ita wajen samawa Peter Obi gurbi a jam’iyyar Labour.
“Lokacin da yake gwamna, Obasanjo ya so ya tsige shi; Na taimaka ta hanyar amfani da rahoton Sahara Reporters wajen fallasa duk makirce-makircen da aka kulla masa."

'Yan Arewa da ke bayan Obi

A wani labarin, Sowore ya yi ikirarin cewa wasu manyan yan Arewa da tsaffin shugaban kasa suna goyon bayan takarar Peter Obi.

Dan takarar na AAC ya lissafa tsaffin shugaban kasa uku na mulkin soja - Olusegun Obasanjo, Ibrahim Babangida da Abdulsalam Abubakar a matsayin 'iyayen gidan' Obi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel