Buratai ya Maka Sowore Kotu, Yayin Da Ya Nemi Diyyar Biliyan N10bn Dan Bata Sunan Shi

Buratai ya Maka Sowore Kotu, Yayin Da Ya Nemi Diyyar Biliyan N10bn Dan Bata Sunan Shi

  • Tsohon hafsan sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya maka mawallafin jaridar Saharar Reporters Omoyele Sowore a kotu bisa zargin buga labaran karya akan shi
  • Omoyele Sowore ya buga wani rahoto da ya alakantar da Buratai da cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ICPC, ta gano biliyoyin kudade a gidansa dake Abuja
  • Buratai ya bukaci kotu ta tursasa Omoyele Sowore ya janye kalaman batanci da yayi akan shi kuma ya fito fili ya bashi hakuri

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Tsohon hafsan sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya maka mawallafin jaridar Saharar Reporters Omoyele Sowore a gaban wata babbar kotun tarayya dake birnin tarayya bisa zargin buga labaran karya akan shi. Rahoton LEADERSHIP

Buratai na neman diyyar Naira biliyan 10 ne saboda a cewarsa, Sowore, mawallafin jaridar Sahara Reporters, ta yanar gizo da ke Amurka, ya alakanta shi da wani rahoto da ke cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ICPC, ta gano biliyoyin kudade na gida da na kasashen waje a wani gida sa dake Abuja.

Kara karanta wannan

Ba gaskiya bane: Gwamna dan rashawa da Buhari ya yiwa afuwa ya musanta batun yin takara a 2023

A karar da Buratai ya shigar mai lamba FCT/HC/CV/252/2022 ta hannun lauyansa, Dokta Reuben Atabo, SAN, yace ya kamata a hana Sowore da gidan jaridar sa ci gaba da buga duk wani labarin batanci game da Buratai

Buratai
Buratai ya Maka Sowore Kotu, Yayin Da Ya Nemi Diyyar Biliyan N10bn Dan Bata Sunan Shi FOTO LEADERSHIP
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan ya bukaci kotu ta tursasa Sowore ya janye rubutun batanci da ya wallafa a shafin Sahara reporters a ranar 23 ga watan Yuni 2022 mai taken ‘Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, ICPC ta bankado biliyoyin kudade don yakar Boko Haram a gidan Babban hafsan sojin kasa Buratai

Kuma lauyan ya bukaci kotu ta tursasa shi yafito fili ya ba Tukur Buratai hakuri kuma bayan haka dolen shi ya buga a cikin manyan jaridun kasar guda biyu da kuma a dandalin intanet.

Kara karanta wannan

Buhari: Da zarar an yi kidaya a 2023, za a samu mafita ga matsalar rashin tsaro

Barayin Fasinjan Jirgin Kasa sun Yaudari Gwamnati Bayan sSakin Iyalansu

A wani labar kuma, Fadar shugaban kasa ta ce, yan ta’adan da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasa dake jigila daga Abuja zuwa Kaduna sun yaudari gwamnati. Rahoton BBC

A lokacin da suke tattaunawa da gwamantin sun mata alkawarin cewa zasu sako fasinjojin jirgin kasa da suka sace idan ta biya musu bukatun su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa

Online view pixel