'Yan Takarar Gwamnan AAC Sun Yi Watsi da Dan Takarar Su Na Shugaba Kasa, Sowore

'Yan Takarar Gwamnan AAC Sun Yi Watsi da Dan Takarar Su Na Shugaba Kasa, Sowore

  • Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC ya gamu da tasku da koma baya daga ‘yan takararsa na gwamna
  • ‘Yan takarar gwamna 12 suka bayyana juya baya ga Omoyele Sowore saboda wasu dalilai da suka bayyana
  • Saura kwanaki kalla 12 a yi zabe a Najeriya, Sowore da Peter Obi sun samu koma bayan mabiya

Kasa da kwanaki 12 a yi zaben shugaban kasa, akalla ‘yan takarar gwamna 12 ne a jam’iyyar AAC suka yi watsi da dan takararsu na shugaban kasa, Omoyele Sowore, Vanguard ta ruwaito.

Sun yi zargin cewa, Sowore bai da tabarau na tantancewa da kwarewa a fannin dimokradiyya da iya shugabancin da zai kai shi ga gaje kujerar Buhari a zaben bana.

‘Yan takarar da suka sauya shekan sun hada da; Iboro Robert Oru na Akwa Ibom; Aliyu Ahmed na Kwara; Ray Ken na Enugu; Mojeed Kehinde Okedara na Oyo; Aliyu Adamu na Gombe da sauransu.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Atiku Abubakar Ya Roki Jami’an Tsaro Su Cafke Tsohon Jigon PDP

'Yan takarar gwamna sun saki layin SOWORE
'Yan Takarar Gwamnan AAC Sun Yi Watsi da Dan Takarar Su Na Shugaba Kasa, Sowore | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Dan takarar gwamnan jihar Akwa Ibom, Robert ya yi magana da manema labarai, inda yace Sowore bai da cikakken kwarewa da sanin dimokradiyya, domin ya ba kansa takarar shugaban kasa kuma shine shugaban jam’iyyar AAC na kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake wanke hannunsa a tafiyar Sowore, Robert ya ce, nan ba da jimawa ba zai bayyana dan takarar da yake goyon baya a zaben bana.

Ya kamata Buhari ya kawo mafita ga matsalolin da ke damun ‘yan Najeriya

A bangare guda, dan takarar gwamnan ya yi kira shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta daukar mataki game da halin da ‘yan Najeriya ke ciki a halin yanzu.

Ya koka da cewa, ‘yan Najeriya na siyan man fetur a karin sama da kaso 400% na yadda suke siya a shekarun baya, Blue Print ta tattaro.

Kara karanta wannan

2023: Dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar su Peter Obi ya kama hanyar Tinubu da Ganduje

Hakazalika, ya koka da yadda kasar ke fuskantar hauhawar farashin kayayyaki babu gaira babu dalili.

A bangare guda, ya bayyana rashin jin dadinsa ga yadda babban bankin Najeriya (CBN) ya tsoma jama’a cikin tashin hankalin karancin kudi

Peter Obi ya rasa mabiyansa a Kudu maso Yamma

A wani labarin kuma, kun ji yadda aka yi bikin yaka tambarin jam’iyyar Labour a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Wannan babbar barazana ce ga ci gaban siyasan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi.

Dama yankin Kudu maso Yamma ya kasance gida dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel