Fadar shugaban kasa
A shekarar 2024 gwamnatin Bola Tinubu ta saye sabon jirgin shugaban kasa. Rahoto ya nuna cewa an kai jirgin gyara kasar Afrika ta Kudu domin a masa kwaskwarima.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa bai ɗauki matakai masu tsauri don jefa ƴan kasa cikin ƙunci ba sai don samun ci gaba mai ɗorewa a Najeriya.
Shugaba Tinubu ya gana da Gwamna Sheriff a fadar Aso Villa 'yan kwanaki bayan komawarsa APC. Wannan ce haduwar Tinubu da gwamnan Deltan bayan barin PDP.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci wasu daga cikin jihohin Najeriya bayan hawansa mulki. Wasu daga cikin ziyarorin ya yi su ne don kaddamar da ayyuka.
Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta amince da wasu muhimman ayyuka da za su laƙume kudi sama da Naira biliyan 750.
Tinubu ya rantsar da shugaban NASC, kwamishinoni 12, da sakatarori biyu gabanin taron majalisar zartarwa. Kwamishinoni sun fito daga shiyoyi shida.
Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya shawarci Atiku Abubakar ya haƙura da neman zama shugaban kasa domin babu alamar Allah zai ba shi damar shugabanci.
Rahoton hukumar kula da albashi na 2007 ya nuna cewa shugabannin kasa na samun fiye da Naira miliyan 10 a kowace shekara, alawus din mazaba kadai na kai N8m.
Hakeem Baba Ahmed ya ce ya yi bayani kan alakar da ke tsakanin Bola Tinubu da Kashim Shettima. Ya ce ya ajiye aiki ne saboda babu abin da yake a Villa sai zama.
Fadar shugaban kasa
Samu kari