Makusantan Buhari Sun Fara Janye Wa Suna Komawa Wurin Tinubu

Makusantan Buhari Sun Fara Janye Wa Suna Komawa Wurin Tinubu

  • Fadar shugaban ƙasa ta ce wasu ma'aikatan Buhari sun fara canja wuri, sun koma wurin zababben shugaban kasa, Bola Tinubu
  • Mallam Garba Shehu, ya ce wannan ba sabon abu bane domin ɗabi'a ce ta ɗan adam ya sauya wuri don cimma burinsa
  • Ya ce haka ta faru a lokacin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan amma akwai ɗan banbanci a tsakani

Abuja - Kakakin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Mallam Garba Shehu, ya bayyana cewa wasu daga cikin hadiman shugaba Buharu sun fara janye jiki suna komawa tsagin shugaba mai jiran gado, Bola Tinubu.

Shehu ya ayyana irin wannan halayyar da wasu ma'aikatan gwamnatin Buhari ke nuna wa a halin yanzu da, "Ɗabi'ar halittar ɗan adam."

Tinubu da Buhari.
Makusantan Buhari Sun Fara Janye Wa Suna Komawa Wurin Tinubu Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

A cewarsa, abu ne da kowa ya sani wannan ɗabi'ar mutane ce amma yadda hadimai ke janye wa suna komawa wurin gwamnati mai jiran gado ya banbanta da wanda ya faru a lokacin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Halarci Taron Zababɓen Gwamnan APC, Ya Yi Magana Mai Jan Hankali, Bayanai Sun Fito

Kakakin shugaban kasan ya ce akwai banbanci janye jikin baya da na yanzu saboda Jonathan ya nuna kishin ƙasa ne a wancan lokacin, kamar yadda Punch ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shehu ya ce:

"Lokacin da Jonathan ya mika wa Buhari mulki ranar 29 ga watan Mayu, 2015 a Eagle Square, akwai wani abun wulakanci da ya biyo baya."
"Ba sai na ja da nisa ba, yan Najeriya sun ta yaɗa tsohon shugaban ƙasa a lokacin saboda da ya isa filin jirgi, jami'an tsaro suka hana shi amfani da ɓangaren shugaban ƙasa, da sauran abubuwan da suka faru."

Shin ma'aikatan Buhari sun fara janye masa jiki?

Daily Trust tace Yayin da aka tambaye shi ko ma'aikatan Buhari sun fara canja mubaya'arsu suna komawa wurin Tinubu, Mallam Garba Shehu ya ce:

"Ba zaka iya canja ɗabi'ar dan adam ba amma a halin yanzu wanda ake ya yi shi ne shugaban kasa mai jiran gado, don haka dole mutane zasu koma su kewaye shi."

Kara karanta wannan

To Fa: Gwamnan Arewa Na PDP Ya Magantu Kan Yuwuwar Ya Koma Jam'iyyar APC

"Amma da banbanci da abubuwan da suka faru lokacin Jonathan saboda mutane baki ɗaya suka yi ƙaura suka bar wurinsa don kawai ya nuna kishin ƙasa ya karɓi rashin nasara."

Kwankwaso Ga Yan Siyasa: Ku Daina Satar Kuɗin Talakawa, Ku Rika Gina Al'umma

A wani rahoton na daban Rabiu Musa Kwankwaso, ya roki 'yan siyasa su maida hankali wajen gina mutane maimakon wawure kuɗin gwamnati..

Tsohon gwsmnan ya kuma halarci taron lakcar da aka shirya a wani ɓangaren bikin rantsar da zababben gwamnan jihar Neja na APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel