Hukumar Sojin Najeriya
An yi ta yada rahotannin cewa akwai yiwuwar yunkurin juyin mulki a fadar shugaban kasar Najeriya a daren jiya Lahadi 25 ga watan Faburairu a birnin Abuja.
Sojojin rundunar Operation Whirl Stroke sun yi nasarar kubutar da mutum 13 da aka yi garkuwa da su yayin da muyagun ke kan hanyar kai su jihar Adamawa daga Imo.
Rundunar soji ta koka kan yadda kamfanin wuta ya jefa su cikin duhu wanda ke neman jawo matsala a barikoki inda ta ce gawarwaki sun fara rubewa dalilin haka.
Yayin da wasu 'yan Najeriya ke fatan a yi juyin mulki a kasar, Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce rundunar za ta dauki mataki kan masu fatan haka.
Jirgin rundunar sojin NAF ya yi nasarar sheƙe kwamandoji uku na ƙungiyar ta'addancin ISWAP a wani ruwan bama-bamai da ya kai mafakarsu a jihar Borno.
Jami'an rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar halaka ɗan bindiga ɗaya, sun kakkabe sauran daga maboyarsu daga dajin Yadi a jihar Kaduna ranar Talata.
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke wasu sojojin boge guda biyu wadanda ake zargin sun yi barazanar kashe wani mutum da wuka a yankin Isolo da ke jihar.
Wasu miyagun ƴan bindiga sun toshe babban titin Gusau zuwa Sakkwato, su. yi awon gaba da matafiya daga motoci biyu da yammacin ranar Talata a yankin Maru.
Miyagun ƴan bindiga sun kashe mutum shida yayin da suka kai farmaki kauyen Ƴar Kasuwa da wasu kauyuka biyu a karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.
Hukumar Sojin Najeriya
Samu kari