Labaran tattalin arzikin Najeriya
Bankin Duniya ya ba Najeriya bashin dala miliyan 500 domin karfafa kamfanonin rarraba wutar lantarki (Discos). Kamfanin TCN ya yi bayanin yadda za a kashe kudin.
Tsohon dan majalisar wakilai, Dachung Bagos ya gargadi gwamnatin tarayya kan tulin basussukan da take karbowa yana mai tambayar inda za a samo kudin da za a biya,
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da buƙatar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu wanda ya nemi a ba shi damar ya sake karɓo rancen kudi daga waje.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya gabatar da kasafin kudin 2025 na Naira tiriliyan 3 ga majalisar dokokin jihar Legas. Kasafin ya mayar da hankali kan dorewar ayyuka.
A wannan labarin, za ku ji gwamnatin tarayya ta bayyana matakin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki bayan fara kaddamar da manufofin Tinubu a kasar.
Gwamna Inuwa Yahaya ya gabatar da kasafin kudin N320bn na shekarar 2025. Bangaren noma da ilimin manyan makarantu, da muhalli sun samu kaso dan kadan.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya nemi gwamnatin tarayya da ta yi wa yan Najeriya bayanin kan rashin cin moriyar arzikin da ake samu a bangaren gas da fetur.
Ministan kudi da harkokin tattalin arziki, Wale Edun ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu na iya bakin kokarinta wajen kyautata rayuwar ƴan Najeriya.
Gwamna Dikko Umaru Radda zai raba tallafin Naira biliyan 5 ga mata a jihar Katsina. Za a raba tallafin N5bn ne domin farfaɗo da kananan sana'o'in mata a Katsina.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari