Bidiyon Yadda Wani Dan Najeriya Ya Tsula Wa Dan NEPA Bulala da Adda Ya Jawo Cece-Kuce

Bidiyon Yadda Wani Dan Najeriya Ya Tsula Wa Dan NEPA Bulala da Adda Ya Jawo Cece-Kuce

  • Wani dan Najeriya ya yiwa dan NEPA rashin mutunci ta hanyar farmakarsa yayin da ya kai ziyarar aiki a unguwar
  • Da farko fusataccen mutumin ya janye tsanin da dan NEPA ke kai daga jikin falwaya, sai kuma ya bi shi da adda da gudu
  • Bai tsaya daga nan ba, mutumin ya bi jami’in NEPA da adda, mutane da yawa sun taru suna kallo basu ce komai ba

An samu cece-kuce da rikici yayin da wani dan Najeriya ya fusata ta fatattaki wani ma'aikacin kamfanin wutar lantarki.

A wani bidiyon da aka yada a TikTok, mutane sun yi kallo yayin da mutumin ke jawo dan NEPA daga tsanin yanke wuta.

Da farko, ya fara ne da dauko adda kana ya tunkari falwaya kamar dai zai duba wani bau. Yayin da cacar baki ta barke tsananinsu, sai ya farmaki mutumin da ke kan tsani.

Kara karanta wannan

An Yi Dirama Yayin Da Wani Ya Taho Ofishin CBN Na Kano Dauke Na Tsaffin Kudi N50m Cikin Buhu, Bidiyon Ya Bazu

Bayan lakada masa duka da adda, dan NEPA ya arce a guje don tsira da ransa, inda mutumin ya ci gaba da binsa a guje.

Dan NEPA ya sha dakyar a hannun dan Najeriya
Bidiyon Yadda Wani Dan Najeriya Ya Tsula Wa Dan NEPA Bulala Ya Jawo Cece-Kuce | Hoto: @gaboncho1.
Asali: TikTok

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutumin da ya yada bidiyon a TikTok ya gargadi ‘yan NEPA da su bar mutane, wannan lokacin kowa a fusace yake.

Kalli bidiyon

Martanin jama'a

psalmsam:

"Dan NEPA ya iya gudu... cewa ya yi bari na fece...”

Mindmorpher:

"Ka dawo mana.. Ka zo ka dauki tsaninka.. Me yasa kake guda..?

Climax:

"Ya san gidanka zai iya tattara mutanensa ya zo ya same ka ba komai ne zai faru ka dauko adda ba.”

code to success:

"Na rantse wannan yanzu ya dawo daga banki sai ya same su a gidansa.”

Yadda falwaya ta rikito da wani dan NEPA

A wani labarin kuma, wani ma’aikacin wutar lantarki mai suna Tunde a jihar Legas ya tsinci kansa a asibiti yayin da ya rikito daga saman falwaya yayin gyaran wuta.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari Ya Tona Abin da Ya Jawo Manya Suke Adawa da Tsarin Canza Nairori

A cewar rahotanni, Tunde ya hau saman falwaya ne domin yanke wutar wani lokacin da lamarin ya faru dashi, ya tsince kansa a asibiti babu shiri.

An ruwaito cewa, ya fado ne daidai lokacin da ya gama yanke wutar, lamarin da ya zo masa da tsaiko, abokan aikinsa sun bayyana yadda komai ya faru da yadda suka kai shi asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel