Mu na Shan Wahala: Ranar Nan Rashin Kudi Ya Jawo Mun Gaza Dafa Abinci - Sanata

Mu na Shan Wahala: Ranar Nan Rashin Kudi Ya Jawo Mun Gaza Dafa Abinci - Sanata

  • Orji Uzor Kalu ya na ganin tsarin takaita yawon kudi da canza Nairori da aka kawo sun yi daidai
  • Amma tsohon Gwamnan na jihar Abia ya soki lokacin da aka zaba wajen fito da tsare-tsaren tattalin
  • Sanata Kalu ya bada labarin yadda aka gaza girki a gidansa saboda tsabar karancin kudi a Abuja

Abuja - A ranar Litinin aka ji Orji Uzor Kalu yana kokawa a kan yadda sauya kudi da bankin CBN ya yi, ya jawo shi da iyalinsa suke rayuwa a kunci.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin Channels, Sanata Orji Uzor Kalu ya bada labari kwanan nan an yi ranar da aka gaza dafa abinci a gidansa.

Orji Uzor Kalu wanda ya yi shekaru takwas yana Gwamna a Najeriya ya ce shi ma yana shan wahalar sabon tsarin da Gwamnan CBN ya fito da shi.

Kara karanta wannan

Sanusi II Ya Yi Magana a Kan ‘Habu na Habu’ da Wanda ya Dace Mutane Su Zaba a 2023

Sanatan na Abia ta Arewa ya shiga sahun masu kokawa da tsarin takaita yawon kudi, yana ganin abin daidai ne, amma ba a zabi lokaci mai kyau ba.

Tsarin dai daidai ne, amma - Kalu

“Ka ga tsarin daidai ne, amma ba na ajiye kudi a cikin gidana. Ina shan wahala.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ranar nan Manajan gidana ya fadawa matata a Abuja ba mu da kudin dafa abinci. Matata tayi ta gantali, kuma mu na ciyar da fiye da mutum 250 kullum."

- Orji Uzor Kalu

Orji Uzor Kalu
Sanata Orji Uzor Kalu a Majalisa Hoto: @OUKtweets
Asali: Twitter

Babban ‘Dan siyasar ya fadawa shirin na The 2023 Verdict cewa tsarin tattalin arzikin ya zama matsala gare sa da sauran mutane domin kowa na kuka.

Daily Post ta ce ‘dan majalisar yana ganin canza kudi ba zai jawo APC ta sha kashi a zabe ba. An ji mai rabawa marokan N100, 000 yana cewa bai d a N1000.

Kara karanta wannan

Haba Baba: Gwamnan APC Ya Bi Hanyar Lalama, Ya Aikawa Buhari Wasika kan Canza Kudi

Shari’ar canjin kudi

Mai tsawatarwa a majalisar dattawan kasar ya kuma bayyana cewa zai fi kyau a ce Mai girma Muhammadu Buhari ya yi biyayya ga hukuncin kotun koli.

Orji Kalu yana tare da Gwamnoni da jam’iyyar APC wajen sukar umarnin shugaban kasa na hana amfani da N500 da N1000 a lokacin da ake tsakar shari’a.

"Shiyasa da ni ne a takalmi shugaban kasa kamar yadda na fada maka, zan yi biyayya ga hukuncin kotun koli tayi, ko da daidai ne ko ba daidai ba.
Mai girma shugaban kasa ya yi biyayya ga doka, ya fadawa babban lauyansa ya duba shari’ar."

- Orji Uzor Kalu

Mata masu zaman kansu su na kuka

A wani rahoto kun ji yadda harka ta tsaya cak, canjin kudi da Gwamnan CBN ya yi, ya yi wa karuwanci tasiri inji masu zaman kansu a garin Abuja.

Saboda karancin kudi, ana samun tangarda wajen turawa ‘yan mata kudi a asusun bankinsu, hakan ta sa dole farashin yin lalata da mata ya karye.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari Ya Zolaye Ganduje: Ka Tafi Ka Kai Tsaffin Nairan Ka CBN Idan Na Halas Ne

Asali: Legit.ng

Online view pixel