Karancin Kudi: Dan Najeriya Ya Fito Da Tsofaffin Naira Da Aka Buga Shekara 15 Da Suka Gabata, Bidiyo Ya Yadu

Karancin Kudi: Dan Najeriya Ya Fito Da Tsofaffin Naira Da Aka Buga Shekara 15 Da Suka Gabata, Bidiyo Ya Yadu

  • A yayin da ake cigaba da fama da karancin takardun naira, wani mutum ya fito da tsaffin naira wanda an dade da dena amfani da su
  • Kudaden da mutumin ya fito da su sun hada da tsaffin N50 da aka kirkire su a 1991 da tsaffin N20 na takarda da aka kirkira a 1977
  • Dukkan takardun nairan da ya fito da su an maye gurbinsu da sabbin naira na 'polymer' hakan na nufin ba zai iya amfani da su ba kuma

Wani mutum dan Najeriya ya fito da wasu tsaffin takardun N50 da N20 wadanda an dade da dena amfani da su.

A wani bidiyo da ya wallafa a TikTok, mutumin ya baza takardun nairorin inda mutane suka rika sha'awa suna mamakin inda ya samo su.

Kara karanta wannan

Rikici: Rigima ta barke yayin da fusataccen dan Najeriya ya bi dan NEPA da adda a guje

Tsohon kudi
Dan Najeriya Ya Fito Da Tsofaffin Naira Da Aka Buga Shekara 15 Da Suka Gabata, Bidiyo Ya Yadu. Hoto: TikTok/@070kamaldincmc and Westend61/Getty Images. (hoton mutumin na kwatance ne).
Asali: TikTok

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutumin ya nuna wa al'umma tsaffin takardun nairan ya kuma ce tsaffi ne wadanda aka sauya su a baya.

Dan Najeriya da aka gan shi da tsaffin N50 da N20 ya yi fice

Tsaffin takardun N50 mutumin ya fito da su an kirkire su ne a shekarar 1991. A 2009, an maye gurbinsa da N50 na leda 'polymer'.

Hakazalika, mutumin ya nuna tsaffin N20 wacce gwamnati ta fitar a 1977 daga bisani aka maye gurbinsu da N20 na leda a 2007 wadanda har yanzu ake amfani da su.

Mutumin wanda ya yi magana da harshen Hausa a bidiyon ya ce:

"Toh, Ikon Allah, ga tsohon kudi fa. Tsohon kudin da aka canja a baya."

Yan Najeriya wadanda suka kalli bidiyon a TikTok suna mamakin yadda mutumin ya ajiye kudin tsaf-tsaf.

Kara karanta wannan

An Yi Dirama Yayin Da Wani Ya Taho Ofishin CBN Na Kano Dauke Na Tsaffin Kudi N50m Cikin Buhu, Bidiyon Ya Bazu

Tsaffin kudin da mutumin ya fito suna dauke da sa hannun Joseph Oladele Sanusi wanda shine gwamnan CBN daga 1999 zuwa 2004. @070kamaldincmc.

Martanin yan TikTok

@user684249614938 ya ce:

"Wannan N50 din ya fi N500 namu na yanzu."

@Daniel Stanley ya rubuta:

"Ni mutum ne mai ajiye tsaffin naira da kwandala. Zan so in siya daga wurinsa."

@user1622851006768 ya ce:

"Ina da irin wannan kudin har yanzu."

@goodnewsltah ya ce:

"Wannan shine lokacin da naira ke da daraja..."

Kano: An kwashi yan kallo yayin da wani mutum ya isa ofishin CBN da buhanan tsaffin kudi

A wani rahoton wani bidiyo da ke nuna wani mutum tare da mukarrabansa dauke da buhuna na tsaffin kudi a babban bankin Najeriya, CBN, na Kano ya dauki hankulan mutane.

Mutumin yayin amsa tambayoyi da jami'an banki ke masa ya ce kudin nasa na kuma shi dan kasuwa ne mai sayar da fulawa kan sari a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel