Haba Baba: Gwamnan APC Ya Bi Hanyar Lalama, Ya Aikawa Buhari Wasika kan Canza Kudi

Haba Baba: Gwamnan APC Ya Bi Hanyar Lalama, Ya Aikawa Buhari Wasika kan Canza Kudi

  • Rotimi Akeredolu ya rubuta wasika yana neman a canza tsarin canjin kudi da bankin CBN ya kawo
  • Gwamnan Ondo ya ce sauya kudin da ake kokarin yi ya zo da matsalolin da za su iya shafan zaben bana
  • Ganin yadda kananan ‘yan kasuwa da marasa karfi ke ciki, Akeredolu ya roki a dawo da tsohon kudi

Ondo - Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, ya roki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bar tsofaffin kudi su cigaba da yin aiki.

Legit.ng Hausa ta fahimci Rotimi Akeredolu ya rubuta wasika da kan shi zuwa ga shugaban kasa game da canjin takardun kudi da aka fito da shi.

Ganin halin da mutane su ka shiga a dalilin karancin kudi, da kuma zanga-zangar da ya barke a wasu jihohi, Gwamnan ya aikawa Buhari wasika.

Kara karanta wannan

Ganduje ya shirya yaki, ya fadi yadda zai hukunta bankin da bai karbar N500, N1000

Jaridar The Cable ta ce Akeredolu SAN yana tsoron rigingimun da ake fama da su yau, za su iya shafar babban zaben da ake shirin yi a kasar nan.

Tsarin bai yi amfani ba - Gwamna

Gwamnan ya nuna tsarin da bankin CBN ya kawo bai haifar da ‘da mai ido ba, a cewarsa rashin lissafi da amfani da bayanan karya suka jawo hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai girma Gwamnan yana ganin da gangan aka lauya alkaluma saboda a dabbaka tsarin.

Gwamnan Ondo
Rotimi Akeredolu da tutar APC Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

A rahoton TVC, Akeredolu ya ce canjin kudi ya jefa kananan ‘yan kasuwa da marasa karfi cikin wahala, ya bukaci a dawo da tsofaffin Nairori.

Akwai fushi tattare da mutane a kasar nan. Bai kamata a rika yi wa tsarin sauya kudi kallon wata dabarar karbe dukiyar mutane a bankuna ba.

Jawabin Gwamnan jihar Ondo

Kara karanta wannan

El-Rufai Ya Yarda da Ganduje, Ya Jadadda Kutun-Kutun din da Buhari Yake Shiryawa

"Ina mai ikirari da babban murya cewa abubuwan da suke faruwa a kasar nan a yau sun nuna lallai tsarin nan bai haifar da ‘da mai ido ba.
Saboda haka ina kira ga shugaban Najeriya ya canza halin rudani na babu gaira-babu dalilin da aka shiga yayin da kotun koli take shari’a.
Ina mai kira ga shugaban kasa ya kyale ayi amfani da tsofaffi da kuma sababbin kudi tare har sai lokacin da zaman lafiya ya dawo kasar nan.
Wannan zai zama tukwuicin ban-kwana da zai yi wa mutanen kasarsa, musamman marasa karfi da mummunan tsarin ya fi taba su.

- Rotimi Akeredolu

Asali: Legit.ng

Online view pixel