Canza Kudi: Ministoci Sun Sabawa Junansu a Zargin Buhari da Sabawa Umarnin Kotu

Canza Kudi: Ministoci Sun Sabawa Junansu a Zargin Buhari da Sabawa Umarnin Kotu

  • Raji Babatunde Fashola SAN bai ganin Muhammadu Buhari ya yi wa kotun koli rashin biyayya
  • Irinsu Festus Keyamo SAN sun ce Shugaban kasa ya bijirewa hukuncin kotu ga canme dajin kudi
  • Babban Ministan ayyuka da gidaje yana da ra’ayin cewa umarnin Buhari bai ci karo da na kotu ba

Abuja - Ministan ayyuka da gidaje na kasa, Raji Babatunde Fashola bai yarda da takawaransa, Festus Keyamo a kan batun shari’ar canjin kudi ba da kotun koli tayi ba.

Raji Babatunde Fashola a wata hira da ya yi da tashar talabijin TVC a karshen makon jiya, ya nuna shugaban kasa bai fito na fito da kotun kolin kasa ba.

Karamin Ministan ayyuka, Festus Keyamo da wasunsu su na ganin cewa kin bada dama ayi amfani da N500 da N1000 ya sabawa hukuncin kotun koli.

Kara karanta wannan

Sanusi II Ya Yi Magana a Kan ‘Habu na Habu’ da Wanda ya Dace Mutane Su Zaba a 2023

Babatunde Fashola wanda shi ma ya kai matsayin SAN a Lauya, ya musanya wannan batu, ya ce umarnin shugaban kasar bai sabawa na Alkali ba.

Buhari ya tausayawa mutane - Fashola

Tsohon Gwamnan na jihar Legas ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya dauki wannan mataki ne saboda ya rage radadin da 'Yan Najeriya ke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Vanguard ta rahoto cewa Tunde Fashola yana ganin akwai bukatar a duba tsarin canjin kudi, amma ya ce Shugaba Buhari bai yi wa kotu rashin da'a ba.

Buhari a taron magabata
Buhari a taron magabata Hoto: Buhari Sallau Online
Asali: UGC

Tunde Fashola ya ce fahimta fuska ce

A tsarin mulkin farar hula, Ministan tarayyar ya ce akwai damar da za a samu ra’ayi dabam-dabam ta yadda mutane za su rika sabawa juna cikin mutunci.

Ministan yake cewa yi wa kotu rashin kunya tana iya daukar ma’anoni da-dama, ya nuna akwai bukatar a ji hukuncin karshe da kotu za ta yanke tukuna.

Kara karanta wannan

Na Kadu Da Jin Yadda Gwamnonin APC Ke Caccakar Buhari Kan Sauya Kudi, Kwankwaso

Fashola ya nuna ko da daukar matakin zai zama tamkar yin karon-tsaye, idan hakan ya taimakawa 'Yan kasar, to akwai yiwuwar a sasanta a wajen kotu.

This Day a rahotonta, ta ce Fashola yana da ra’ayin cewa ganin yadda Gwamnonin CBN ke shiga matsala a duk lokacin zabe, akwai bukatar ayi nazari.

A cewar Ministan, wasu dalilan da Godwin Emefiele ya bada na canza kudi sun sabawa doka.

Wa zai lashe zaben 2023?

Ku na da labari mun tambayi masu karanta labaranmu game da wanda suke so ya zama sabon Shugaban kasar Najeriya a karshen watan Mayu mai zuwa.

Mutum 5500 suka kada kuri’arsu a zaben da aka shirya kusan kwanaki biyu ana fafatawa. A karshe Jam’iyyun APC da PDP ba su yi farin jini a Twitter ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel