Ku Zabi Shugabanni Masu Gaskiya da Rikon Amana, Malaman Katolika Ga ’Yan Najeriya

Ku Zabi Shugabanni Masu Gaskiya da Rikon Amana, Malaman Katolika Ga ’Yan Najeriya

  • Limaman addinin kirista sun bayyana bukatar a zabe shugabanni na gari masu tsoron Allah a zaben bana
  • Sun shawarci hukumar zabe ta INEC da ta tabbatar da an yi zabe cikin tsanaki ba atre da wata matsala ba
  • A bangare guda, sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo karshen kuncin da ‘yan kasar ke ciki

FCT, Abuja - Limaman kungiyar kiristocin Katolika a Najeriya ra CBCN sun yi kira ga ‘yan kasar da su yi zabi cikin tsanaki a zaben da kasar za ta yi nan da kwanaki biyar.

Sun bayyana cewa, yana da kyau ‘yan Najeriya su zabi shugabanni masu gaskiya, rikon amana da iya mulki a zaben mai zuwa nan ba da jimawa ba, Daily Trust ta ruwaito.

Sun bayyana hakan ne tare da cewa, zaben 2023 wata dama ce ga ‘yan Najeriya su barranta da shaidanu kana su yi zaben shugabanni na gari a kujeru daban-daban na siyasa.

Kara karanta wannan

Karya ne: Fadar Shugaban Kasa ta Karyata Zargin El-Rufai da Ganduje

Cocin Katolika ya fadi dan takarar da yake zo
Ku Zabi Shugabanni Masu Gaskiya da Rikon Amana, Malaman Katolika Ga ’Yan Najeriya | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sun yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da suka fitar karshen wani taron da suka gudanar a cibiyar CSN da ke birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da limaman Katolika ke bukata

An ba manema labarai sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban CBCN Most Rev. Lucius Ugorji, babban limamin Katolika na Owerri da sakataren kungiyar, Most Rev. Donatus Ogun a birnin Adok-Ekiti ta hannun Most Rev. Felix Ajakaye.

Sanarwar ta ce:

“Kuri’unmu na da daraja; dole za mu yi amfani dasu da kyau, muna kira ga duk wadanda suka cancanta su fita kwai da kwarkwata su zabi masu tsoron Allah, masu gaskiya, wadanda suka dace kuma masu amana don goben Najeriya.
“Muna kira ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da jami’anta su tabbatar aikinsu a ilahirin zabe ya zama a bayyane, da gaskiya kuma ba za a iya tankwara su ba.”

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Najeriya sun gaji da Buhari, matar Atiku ta yi bayanai masu daukar hankali

A kawo karshen matsalar tattalin arziki, inji limaman Katolika

A bangaren kuncin tattalin arziki da ake fuskanta a kasar, limaman kiristan sun yi kir ga gwamnatin tarayya da sauran wadanda abin ya shafa da su wadatar da kasar da sabbin kudi, rahoton Vanguard.

A cewarsu, hakan ne zai taimakawa ‘yan Najeriya wajen rage radadin halin da suke ciki na talauci da tashin hankali.

A halin da ake ciki, shugaba Buhari ya roki 'yan Najeriya su zabi Tinubu, domin a cewarsa, Tinubu ne zai iya daurawa daga inda ya tsaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel