Wata Mata Mai Juna Biyu Ta Kwararo Addu'a Ga Mutumin Da Yayi Mata Kyautar Sabbin Kuɗi

Wata Mata Mai Juna Biyu Ta Kwararo Addu'a Ga Mutumin Da Yayi Mata Kyautar Sabbin Kuɗi

  • Bidiyon wata mata mai suna biyu da ta samu kyautar sababbin kuɗi ya sosa zuciyoyi
  • Matar wacce cikin sa'a ta haɗu da wanda yayi mata kyautar ta shiga cikin tsananin farin ciki
  • Mutane da dama sun yabawa mutumin bisa taimakon matar mai juna biyu da yayi, inda su kayi ta masa fatan alheri

Wata mata ƴar Najeriya ta haɗu da sa'a bayan wani wanda bata sani ba ya gwangwanje ta kyautar sababbin kuɗi.

A wani bidiyo da wani amfani da sunan @dexycreation ya sanya a TikTok, ya nuna lokacin mutumin ya haɗu da matar a gidanta inda ya gano cewa tana ɗauke da juna biyu.

Matar Aure
Wata Mata Mai Juna Ta Kwararo Addu'a Ga Mutumin Da Yayi Mata Kyautar Sabbin Kuɗi Asali: Instagram/Dexycreation
Asali: Instagram

Lokacin da ya tambayeta ta faɗi tafi buƙatar a taimaka mata da shi nan take, sai matar ta buɗe baki tace ita da ƴaƴanta suna buƙatar abinci.

Kara karanta wannan

Ana Saura Sati Ɗaya Biki, Amarya Tace Ta Fasa, Ta Bayyana Dalilinta

Bayan juna biyun da take ɗauke da shi, matar tana yara biyu waɗand take ɗaukar ɗawainiyar su. Tace mijinta ya kwana biyu bai samu aikin da zai yi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai kawai mutumin ya bata kyautar tsabar kuɗi wanda ya sanya ta cikin matuƙar farin ciki.

Tsananin daɗi ya sanya ta miƙe tsaye tana ta ƙwararowa mutumin addu'o'i, inda ta roƙi ubangiji ya biya masa buƙatun sa.

Bidiyon ya taɓa zuciyoyi sosai wanda ya sanya mutane suka yi ta maganganu masu kyau a kansa a Instagram.

Ga kaɗan daga ciki:

@christianegwuatu3133 ya rubuta:

"Addu'ar daga cikin zuciyarta take kwararota."

@babyteegram ta rubuta:

"Yadda kake taimakon mutane, Allah zai taimake ka."

@curalyon ya rubuta:

"Yakamata ace akwai tsarin ƙayyade iyali kyauta ga talakawa marasa ƙarfi."

@easybusy_sharp ya rubuta:

"Allah yayi maka albarka ɗan'uwa. Sai da nayi kuka bayan kallon wanann. Akwai yunwa sosai a Najeriya."

Kara karanta wannan

Gamo Da Katar: Budurwa Ta Fashe Da Kukan Daɗi Bayan An Gwangwajeta Da Miliyoyi

@john_ajegi ya rubuta:

"Ina jindaɗi sosai saboda abin alherin da kake yi. Akwai takaici ganin irin wahalar da mutane ke sha a yanzu."

Kukan Daɗi: Budurwa Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Samu Kyautar Maƙudan Kuɗi

A wani labarin wata budurwa ta fashe da kukan daɗi bayan an yi mata wata kyautar da ba zato ba tsammani.

Tsananin farin ciki ya sanya budurwar ɓarkewa da kuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel