Dalilin da Yasa Muka Maka CBN da Buhari a Kotun Koli, El-Rufai Ya Magantu Kan Dokar Kudi

Dalilin da Yasa Muka Maka CBN da Buhari a Kotun Koli, El-Rufai Ya Magantu Kan Dokar Kudi

  • Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana dalilin da yasa gwamnoni suka maka shugaba Buhari da CBN a kotu
  • Ya ce gwamnoni sun ba Buhari shawari ya ki dauka, don haka suka yanke shawarin daukar matakin doka
  • El-Rufai ya ce bai yi hakan don tozarta Buhari ba, ya yi ne don tabbatar da mutuncinsa ya tsira a kasa

Jihar Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna ya yi martani ga masu sukarsa game da kai gwamnatin tarayya kotu kan batun da ya shafi sabbin Naira na ka’idojin CBN.

Gwamnan ya bayyana cewa, wasu daga cikin gwamnonin APC sun maka CBN da Buhari a kotu ne saboda an ki jin shawarinsu, rahoton Daily Trust.

Idan baku manta ba, gwamnonin APC, ciki har da El-Rufai sun ce basu amince da wa’adon daina amfani da tsoffin kudi da CBN ya sanya ba.

Kara karanta wannan

Na Kadu Da Jin Yadda Gwamnonin APC Ke Caccakar Buhari Kan Sauya Kudi, Kwankwaso

Dalilin da yasa aka maka Buhari da CBN a kotu, El-Rufai
Dalilin da Yasa Muka Maka CBN da Buhari a Kotun Koli, El-Rufai Ya Magantu Kan Dokar Kudi | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

An sauya kudi a Najeriya, an shiga matsala

A baya CBN ya sauya fasalin N200, N500 da N1000 tare da sanya ranar 10 ga watan Faburairu a matsayin ranar karshe na kashe tsoffin kudaden.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wannan yasa su El-Rufai suka tafi kotun koli tare da neman kotun ta tursasa CBN ya tsawaita wa’adin kashe tsoffin kudin, rahoton Vanguard.

Da yake martani ga masu cewa gwamnonin tare da cewa suna yi ne don cimma wata bukata ta kashin kai, ya ce jama’a basu fahimci halin da ake ciki ba.

Matsayin gwamna daban, na shugaban kasa daban

Da yake zantawa da RFI Hausa, ya ce masu sukarsa basu san abin da dokar Najeriya ta tanadar wa gwamna ba da kuma shugaban kasa.

A cewarsa:

“Sau nawa ina magana gake da rashin tsaro, shekara uku ina ba da shawarin kada a yi sukhu da ‘yan ta’adda, a kashe su kawai, amma yanzu mutane sun mata abin da na fada kuma suka fara cewa ban yi martani kan ka’idar?”

Kara karanta wannan

Mutanen Kaduna Sun Yi Watsi Da Umurnin El-Rufai, Suna Ta Rububin Kai Tsaffin Kudadensu CBN

Ya kuma yi bayani game da yadda gwamnoni ke shawartar gwamnatin tarayya kan matsalolin tsaro, ciki har da batun harin ‘yan bindiga kan jirgin kasan Abuja-Kaduba.

Har yanzu ana fama da karancin sabbin Naira a Najeriya, amma an ga wasu ‘yan kasuwa na karbar tsoffin kudi a wurin taron gangamin tallata Tinubu a jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel