Sanatar Arewa Ta Tuna da Mutanen Mazabarta, Ta Raba Masu Buhunan Kayan Abinci a Ramadan

Sanatar Arewa Ta Tuna da Mutanen Mazabarta, Ta Raba Masu Buhunan Kayan Abinci a Ramadan

  • Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti, ta farantawa mutanen mazaɓarta yayin da ta raba tirelolin kayan abinci
  • Natasha ta bayyana cewa ta yi haka ne saboda matsanancin matsin tattalin arzikin da mutane ke fama da shi a sassan ƙasar nan
  • A cewarta, kowane mutum a mazaɓar ka iya samun wannan tallafi ba tare da la'akari da banbancin siyasa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kogi - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar mazaɓar Kogi ta Tsakiya a majalisar dattawa ta yunƙuro da nufin taimakawa mutanen mazaɓarta.

Natasha ta raba adadi mai yawa na kayan abinci a mazaɓarta domin rage wa iyalai raɗadin hauhawar farashin kayan abinci a ƙasar nan.

Sanata Natasha.
Natasha ta waiwayi al'ummar Kogi ta Tsakiya da tallafin kayan abinci Hoto: OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da jam'iyyar PDP ta wallafa a manhajar X wanda aka fi sani da Twitter a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta faɗi ranar da za a kammala ɗaukar sababbin ma'aikata a hukumar FFS

Abubuwan da ta raba sun haɗa da buhunan shinkafa, wake, da gero guda 7,200, wadanda aka raba zuwa gundumomi 57 da ke fadin kananan hukumomi 5 a mazaɓar Kogi ta Tsakiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa da ta fitar, Sanata Natasha ta jaddada cewa ba za a nuna banbanci ba wurin rabon wannan tallafi, kowa ka iya amfana.

"Tallafin na dukkan mutanen mazaɓata ne ba tare da duba wace jam'iyya mutum yake goyon baya ba," in ji ta.

Waɗanda suka amfana da tallafin Natasha

Daga cikin wadanda suka ci gajiyar wannan rabon akwai kungiyoyi daban-daban na Musulmi da Kirista, direbobi, ƴan acaba da keke, kanikawa, ‘yan fansho, da kuma kabilu daban-daban da suka hada da Hausa/Fulani da Yarabawa.

Sanatar ta bayyana cewa ta shirya yi wa mutanen da suka zaɓe ta hidima fiye da wannan tallafin na lokaci ɗaya kuma ba shi ne na ƙarshe ba.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa na shirin ɗage dakatarwan da ta yi wa Sanata Abdul Ningi, ta faɗi dalili

Natasha Akpoti ta ce:

"Zan ci gaba da yin iya bakin kokarina wajen ganin na kawo musu mafi kyawun ribar dimokuradiyya."

Kuros Riba za ta ɗauki malamai 6000

A wani rahoton kuma Gwamnatin Kuros Riba karkashin Gwamna Baseey Otu za ta ɗauki sababbin malamai 6000 domin cike giɓin rashin isassun malamai a makarantu

Kwamishinan ilimi na jihar, Stephen Odey, ne ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a ofishinsa ranar Talata, 2 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel