Sauki Ya Zo: Bankin CBN Ya Karya Farashin Dala a Najeriya, Ya Aike da Saƙo Ga Ƴan Canji

Sauki Ya Zo: Bankin CBN Ya Karya Farashin Dala a Najeriya, Ya Aike da Saƙo Ga Ƴan Canji

  • Babban bankin Najeriya ya ƙara karya dala yayin da ya siyar da $10,000 ga kowane ɗan canji kan farashin N1,251
  • A wata sanarwa, CBN ya umarci dukkan ƴan canjin su ƙara kashi 1.5% kan farashin da aka siyar masu
  • Wannan mataki dai zai taimaka wajen saukar farashin kayayyaki wanda ƴan Najeriya ke ta kuka a kansa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya sake karya farashin Dala yayin da ya fara siyar da ita ga halastattun ƴan canji kan farashi mai rahusa.

Babban bankin ya tura wata takardar sanarwa ga ƴan canji (BDC), inda ya sanar da su cewa CBN ya siyar wa da kowane ɗaya daga cikinsu $10,000 kan farashi N1,251/$.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya shiga sabuwar matsala kan zargin alaƙa da ƴan bindiga, bayanai sun fito

Canjin kuɗi.
CBN ya sayar da dala ga yan canji a farashi mai rahusa Hoto: CBN
Asali: Getty Images

Nairametrics ta rahoto cewa CBN, a cikin wannan sanarwa, ya umurci kowane ɗan canji BDC da ya sayar da dala ga abokan cinikin da suka cancanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

CBN ya gindaya wa ƴan canji sharaɗi

CBN ya umarci ƴan canjin su sayar da dala ga duk wanda ya cika sharuɗɗa amma kada su sanya ribar da ta zarce kashi 1.5% a saman farashin da aka sayar masu.

A ruwayar Vanguard, sanarwanr ta ce:

"Bisa takardar da muka aiko maku mai lamba TED/DIR/CON/GOM/001/071 dangane da wannna batu, CBN ya amince da sayar da kuɗaɗen ƙasar waje ga halastattun ƴan canji.
“Muna sanar da ku cewa za mu ba kowane ɗan canji $10,000 kan kudi N1,251/$1. Kowane daga cikinku zai siyar da dala ga kwastomomin da suka cancanta kan ƙarin kashi 1.5% fiye da farashin da ya siya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu Ta faɗi gaskiya kan biyan kuɗin fansa yayin ceto ɗaliban Kaduna

- CBN

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan babban bankin ya bayyana cewa ya biya dala 7bn da suka maƙale ga kamfanonin jiragen sama na ƙasar waje.

Gwaman Buni ya agazawa marayu

A wani rahoton na daban Gwamna Mai Mala Buni na Yobe ya kaddamar da rabon tallafin tsabar kuɗi N50,000 ga marayu aƙalla 1,000 a watan azumin Ramadan.

Wannan ba shi ne karo na farko ba domin gwamnan ya maida shirin tallafin marayu a matsayin wani aiki da gwamnatin ke yi duk shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel