Abuja: Farashin Dala Ya Yi Babbar Faɗuwa Lokaci Guda a Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana

Abuja: Farashin Dala Ya Yi Babbar Faɗuwa Lokaci Guda a Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana

  • Ƴan kasuwar canji sun musanta rahoton da ke yawo cewa farashin Dala ya ƙara karyewa, ya koma N1,000 kan kowace $1
  • Wannan na zuwa ne bayan wani rahoto ya karaɗe shafukan sada zumunta cewa Dala ta karye zuwa N1000 a Otal ɗin Sharaton da ke Zone 4 a Abuja
  • A baya-bayan nan ne babban banki CBN ya ce zai sayar da $10,000 ga kowace ɗan canji kan farashin N1251/$1

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ƴan kasuwa masu hada-hadar canjin kuɗi (BDCs) sun musanta rahoton da ke yawo a manhajar X wadda aka fi sani da Twitter cewa Dala ta dawo N1,000.

A cewar ƴan canji, rahoton wanda ya yi iƙirarin farashin Dalar Amurka ya ragu zuwa N1,000 kan kowace Dala ɗaya ba gaskiya bane.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya karbo sabon bashin biliyoyi, Minista ya fadi inda za a jefa kudin

Naira da Dala.
Har yanzu Dala ba ta dawo N1000 ba Hoto: Nurphoto/contributor
Asali: Getty Images

Rahotanni sun karaɗe manhajar X cewa Dala ra rushe zuwa N1,000/$1 a kasuwar ƴan canji da ke birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A safiyar yau a Zone 4 Abuja, daura da Otal din Sheraton, ana siyar da dala a kan N1,000/$1. Abdulsalam BDC yana sayar da ita a farashin N900 ga duk wanda zai sayi sama da $5,000.
"Ana ta rige-rigen sayar da daloli a Zone 4. Dala a kasuwar hada-hadar kudi ta ƴan caji a halin yanzu ta faɗi warwas, ana siyar da ita a farashi mai rahusa fiye da farashin gwamnati," in ji rahoton.

Menene gaskiya kan saukar Dala?

Sai dai wakilin Punch ya tuntubi “Abdusallam BDC” watau Abubakar Abdusallam a ranar Talata a Abuja, kuma ya musanta cewa yana sayar da Dala a kan farashin N900-N1000.

“Muna sayar da Dala a kan farashin N1300/$1, ba N1000 ko N900 ba,” inji shi.

Kara karanta wannan

Gidajen mai sun rage farashin fetur saboda matakin da NNPCL ya ɗauka, an samu bayani

Wani mai amfani da manhajar X, wanda ba a iya tantance sunansa na gaskiya ba, shi ma ya karyata jita-jitar, inda ya bayyana cewa yana Otal ɗin Sheraton kuma ba haka farahin yake ba.

Bankin CBN ya saida Dala a N1200

Idan baku manta ba Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa babban bankin Najeriya ya yi tayin sayar da Dala 10,000 ga kowane ɗan kasuwar canji kan kudi N1,251/$.

Babban bankin CBN yana sa ran kada ƴan canjin su sayar da Dala sama da N1,269/$, ma'ana ribar da za su ɗora ba za ta wuce N18 ba.

CBN ya biya bashin $7bn

A wani rahoton na daban kun ji cewa a kokarin farfaɗo da darajar naira a Najeriya, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya dauki hanyar kawo karshen matsalar.

Bankin karkashin jagorancin Yemi Cardoso ya biya bashin $7bn da ya gada daga tsohon gwamnan bankin, Godwin Emefiele.

Asali: Legit.ng

Online view pixel