An Shiga Sabuwar Matsala, Bashin da China, Faransa, India, Jamus da Japan Ke Bin Najeriya Ya Karu

An Shiga Sabuwar Matsala, Bashin da China, Faransa, India, Jamus da Japan Ke Bin Najeriya Ya Karu

  • Bayanai daga ofishin kula da basuka na kasa ya nuna cewa, bashin da ake bin Najeriya na kasashen waje ya kai $42bn
  • Ga kasashe, DMO ya ce kasar China da wasu kasashen duniya hudu na bin Najeriya bashin da ya kai $5bn
  • Kamar yadda aka yi tsammani, Najeriya cikin bashin China da wasu kasashen duniya dumu-dumu ciki har da Faransa da Jamus

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Ofishin kula da bashi (DMO) ya sanar da cewa, adadin bashin da ake bin Najeriya ya zuwa watan Disamban 2023 ya kai $42.49bn.

Wannan na nuni da raguwar 1.53% ko kuma $664.03m idan aka kwatanta da $43,15 da ake bin Najeriya a matsayin bashin waje a watan Yunin 2023 kafin fara mulkin Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya karyata masu jita-jita cewa ya ware N6bn don ciyar da Kanawa a Ramadana

Wannan sabon rahoto dai ya fito ne daga ofishin na DMO, wanda Legit Hausa ta dauka tare da bin diddiginsa.

Bashin da ake bin Najeriya ya karu
Yadda bashin da ake bin Najeriya ya karu | Hoto: mgkaya
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fashin bakin bashin da ake bin Najeriya na waje

A cewar rahoton na DMO, bashin waje da ake bin Najeriya ya fito ne daga kasashe da bankuna da kungiyoyin waje daban-daban, daga ciki har da IMF, Bankin Duniya, masu zuba hannun jari da kasashe.

A bangaren da ya shafi kasashe, ana bin gwamnatin Najeriya bashin da bai gaza $5.95bn, kamar dai yadda ya bayyana a rahoton.

Wannan kari ne idan aka kwatanta da na watan Yunin 2023, inda kasashen waje ke bin Najeriya akalla bashin $5.51.

Idan aka hada, bashin da kasashen duniya ke bin Najeriya ya kai 14.02% na jumillar bashin ya zuwa watan Disamban 2023.

Kara karanta wannan

Mun tada matattu sama da 50 a cocina bayan tabbatar da mutuwarsu, inji malamin coci Chris

Ga jerin bashin da kasashe ke bin Najeriya

KasasheYunin 2023Disamban 2023Sauyi a lokacin Tinubu
China$4.72bn$5.16bn$440m
Faransa$572.61m$580.13m$7.52m
Japan$57.18m$58.33m$1.15m
India$26.64m$25.94m$0.70m
Jamus$135.26m$125.90m$9.36m

Gwamnati ta biya bashin da ake bin Najeriya

A wani labarin, Babban Bankin Najeriya (CBN) ta biya bashin $7bn da gwamnan bankin, Yemi Cardoso ya gada bayan shigarsa ofis a 2023 daga hannun Emefiele.

Daraktar yada labaran bankin, Hakama Sidi Ali ita ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Laraba 21 ga watan Maris.

An tabbatar da biyan dukkan basukan wanda ake ganin zai iya saka darajar Nairanan ba da dadewa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel