Dala Ta Fadi Sosai Cikin Kwana 2, Naira na Ganin Tasirin Dabarun Gwamnan CBN

Dala Ta Fadi Sosai Cikin Kwana 2, Naira na Ganin Tasirin Dabarun Gwamnan CBN

  • Daga ranar Laraba zuwa Juma’a, Dala ta rasa kimanin 5% a darajarta a kasuwannin bayan fagen ‘yan canji
  • Masu canji sun tabbatar da kimar Naira ta karu da N70 a cikin ‘yan awanni, kimar kudin kasashen waje tana sauka
  • Yemi Cardoso ya ce $1.5bn sun shigo kasar nan, alamun da ke nuna za a iya kawo karshen matsalar karancin Dala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A ranar Juma’a aka ji cewa darajar Naira ta kara tashi a wasu kasuwannin bayan fage da ake cinikin kudin kasashen waje.

Hakan ya na zuwa ne bayan wasu sababbin dabaru da bankin CBN yake kawowa a karkashin jagorancin Micheal Yemi Cardoso.

Bankin CBN
CBN ya taimaka Dalar Amurka ta sauka Hoto: Getty Images, @Cenbank
Asali: UGC

Naira tana tashi a kan Dalar Amurka

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Shugaba Tinubu yayin da ya cika shekara 72

‘Yan canji sun saida Dala a kan N1, 280 a kasuwar bayan fage a ranar Juma’a kamar yadda jaridar The Cable ta fitar da rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan canji da aka samu ya kai 5.19% a kan yadda aka saida kowace Dala kafin nan.

Naira: Dala ta rasa N70 a kasuwa

A ranar Laraba, mutane sun saye Dalar Amurka ne a kan N1, 350. A cikin kwanaki biyu zuwa uku, Naira ta kara kima har da N70.

Tribune ta rahoto Yemi Cardoso ya ce a cikin watan nan, Dala biliyan 1.5 sun shigo Najeriya, hakan ya nuna ana samun nasara.

Dala da kudin waje za su karye?

Baya ga farashin Dala, an ji cewa sauran kudin ketare suna ta sauka a kwanakin nan.

Wani ‘dan canji ya ce kudin kasashen waje suna ta fadi, mutane sun rike kudinsu ba su son su canza domin suna harin babbar riba.

Kara karanta wannan

Abuja: Farashin Dala ya yi babbar faɗuwa lokaci guda a Najeriya? Gaskiya ta bayyana

Legit ta samu labari akwai wadanda suka saye kudin waje kamar Dalar Amurka da niyyar su saida idan darajar Naira ta fadi war-was.

Nawa ake saida Dala a yau?

A kasuwannin canjin da ke garin Legas, ana sayen Dala ne a kan N1, 260 sai kuma ‘yan canjin su saidawa jama’a a kusan N1, 280.

Ribar N20 ne ‘yan canjin suke samu idan sun saida kowace dala a kasuwar bayan fage.

Farashin fetur ya bi Dalar Amurka?

Wasu rahotanni sun nuna cewa NNPCL ya rage farashin fetur, amma an ji labari gaskiya ta fito yayin da kamfanin ya yi magana.

Wannan na zuwa ne yayin da Naira ke ci gaba da farfaɗowa kan Dala a kasuwar canji bayan mummunan karyewar farashin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel