Hukumar Kwastam
Kwanturola na hukumar kwastam da ke yankin Apapa ta jihar Lagas, Abba-Kura ya tabbatar da cewar jami'ansa su goma sun kamu da cutar korona amma dai sun warke.
Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta bayar da izinin kama tsohon Shugaban kwastam din Najeriya, Abdullahi Inde Dikko kan ci gaba da kin halartan zaman kotu domin amsa wani tuhumar damfara da hukumar yaki da rashawa ta ICPC ke yi a
A kokarinsa na rage matsalar cin hanci da rashawa, shugaban hukumar kwastam, Alhaji Hamid Ali ya umarci jami’an hukumar kwastam da su dinga bayyana adadin kadarorinsu a kowanne shekara daga bana.
Rahotanni sun kawo cewa wasu jami’an hukumar kwastam na Najeriya su biyu da aka yi garkuwa dasu sun kubuta daga hannun masu garkuwan bayan kwanaki hudu da sace su.
Hukumar yaki da fasa kauri ta sanar da samun gagarumar nasara a shekarar 2019 inda ta tara makudan kudi da suka kai naira tiriliyan 1.341 a matsayin kudaden shiga daga harajin da take amsa daga watan Janairu zuwa Disamba na shekar
Hukumar yaki da da fasa kauri ta kasa, reshen jahar Neja ta tabbatar da mutuwar wasu jami’anta guda biyu a hannun wasu gungun yan bindiga da suka kai musu farmaki yayin da suke bakin aiki a kan iyakar jahar Neja da jahar Kwara.
Hukumar yaki da fasa kauri, kwastam ta sanar da aniyarta na fara daukan sabbin ma’aikata, inda za ta bude shafinta na yanar gizo don masu neman aikin su daura takardunsu, kamar yadda shugaban hukumar, Hamid Ali ya bayyana.
Col. Hameed Ali, shugaban hukumar kwastam ta kasa ya yi alkawarin fatattakar duk wani jami’in hukumar da ba zai iya dogaro da albashinshi ba, kuma aka kamashi da laifin tara dukiya ta hanyar da ba halas ba...
Hukumar kwastam ta kasa ta hana kai man fetur garuruwan da ke da nisan kilomita 20 tsakaninsu da iyakokin kasar nan. Binciken jaridar Daily Trust ya nuna cewa, garuruwa kusa da iyakokin Najeriya ne suka tsunduma cikin wannan halin
Hukumar Kwastam
Samu kari