Mun Sallami Jami'an Kwastam 2000 Bisa Zargin Cin Hanci Da Rashawa, Hameed Ali

Mun Sallami Jami'an Kwastam 2000 Bisa Zargin Cin Hanci Da Rashawa, Hameed Ali

  • Hukumar Kwastam tayi tankade da rauraya a cikin gidanta karkashin mulkin Kanar Hamid Ali
  • Tsohon Sojan ya ce yanzu sun mallaki jirage sama kuma suna hada kai da hukumar Soji wajen dakile masu fasa kwabri
  • Hukuma kwastam na da hakkin hana shigo da haramtattun kaya Najeriya da kuma shigo da kaya ta barauniyar hanya

Abuja - Kwantrola-Janar na Hukumar Hana Fasa Kwabri watau Kwastam, Kanal Hameed Ali (mai ritaya) ya bayyana irin nasarorin da hukumar ta samu karkashinsa cikin shekaru 7 da suka gabata.

Hameed Ali yace kawo yanzu sun gurfanar da jami'an hukumar sama da 2000 kan zargin rashawa da karban cin hanci kuma sun sallamesu.

Ya kara da cewa yan Najeriya suyi hattara da wadannan hafsoshi kada su damfaresu.

Hameed Ali
Mun Sallami Jami'an Kwastam 2000 Bisa Zargin CIn Hanci Da Rashawa, Hameed Ali Hoto: @abachasam71
Asali: Twitter

Hameed Ali ya bayyana hakan ne yayin a hira da manema labarai a fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

An Yi Watsi Da Sunan Rarara a Kwamitin Kamfen Din Tinubu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

ya ce hukumar Kwastam karkashinsa ta tsananta yaki da fasa kwabri kuma sun sayi sabbin jirage don damke masu shigo da kaya ta haramtattun hanyoyi.

Yace kawo yanku, hukumar ta samu kudi 2.143 trillion a 2022, sabanin 3.019 trillion da aka bukaci tayi.

A cewarsa, an samu wannan nakasu ne saboda har yanzu basu fara karban harajin kamfanonin sadarwa ba.

A cewarsa:

"Mun samu nasarar gano wuraren da ake sata da almundahana shi yasa muka samu nasarar samar da kudin shiga daga N876bn zuwa yau mun samu 2.13tr."

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel