Hukumar Kwastam, NAFDAC, NDLEA sun lalata kwantena 48 na magungunan jabu a Legas

Hukumar Kwastam, NAFDAC, NDLEA sun lalata kwantena 48 na magungunan jabu a Legas

  • Hukumar kwastam ta jagoranci wasu hukumomin gwamnatin tarayya wajen lalata kwantena 48 na magungunan da aka kama marasa inganci da na jabu
  • Kimar magunan da hukumar Kwastam da sauran hukumomin gwamnatin suka lalata ya wuce biliyon daya
  • AGC Usman Dankingari ya ce, miyagun kwayoyi marasa tsari suna kara rura wutar ‘yan fashi da masu garkuwa da matuane

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Legas - A jiya ne hukumar kwastam ta Najeriya ta jagoranci wasu hukumomin gwamnatin tarayya wajen lalata kwantena 48 na magungunan da aka kama, marasa inganci da na jabu a wurin lalata shara na LAWMA da ke Epe a Legas. Rahotan TheNation

Magungunan da aka lalata kimar su ya kai sama da Naira biliyan daya.

Customs
Hukumar Kwastam, NAFDAC, NDLEA sun lalata kwantena 48 na magungunan jabu a Legas FOTO Legit.NG

Wadanda suka lalata kwantena arba'in da takwas 48 na magungunan da aka kama sun hada da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC), hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, da kuma jami’an tsaro na farin kaya (DSS).

Kara karanta wannan

A ina ta samo: Gwamnatin Buhari ta gano N500m a asusun malamar makarantan firamare, ta kwace

Wanda ya jagoranci tawagar kwastam din sune

ACG, Enforcement, Usman Dankingari, Compt. Yusuf Malanta Ibrahim da Kakakin NCS na kasa, DC Timi Bomodi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake jawabi ga manema labarai a wurin da aka lalata, ACG Enforcement, Inspection and Investigation, Usman Dankingari ya ce, miyagun kwayoyi marasa tsari irin wadanda ake lalata su ne ke kara rura wutar ‘yan fashi da garkuwa da mutane da kuma rashin tsaro a kasar nan.

Rundunar sojin Najeriya ta Sauya Fasalin Manyan Hafsoshinta

A wani labari kuma, Rundunar sojin Najeriya ta sauya wa wasu manyan Dakarun ta wanda suka hada da Hafososhi da Kwamandoji wuraren aikin su. Rahoton

BBC Rundunar ta ce, tayi sauye-sauyen ne dan kokarin inganta ayyukan su yayin da matsalar tsaro ta ci gaba da tabarbarewa a Najeriya. Birgediya Janar

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa

Online view pixel