Hukumar NDLEA ta Cafke Mai shekara 75 Gotai-Gotai da Zargin Harkar Kwayoyi

Hukumar NDLEA ta Cafke Mai shekara 75 Gotai-Gotai da Zargin Harkar Kwayoyi

  • NDLEA masu hana fataucin miyagun kwayoyi sun kai ga wani tsoho da ake zargi yana saida kwayoyi
  • An cafke Usman Bokina Bajama wanda mazaunin Mararraban Tola ne a garin Mayo Belwa a Adamawa
  • Jami’an hukumar suna cigaba da karbe kwayoyin Akuskura wanda NAFDAC tace yana yana da hadari

Abuja - Hukumar NDLEA masu yaki da miyagun kwayoyi a Najeriya, tace tayi ram da wani tsoho mai shekara 75 da ake zargi yana harkar kwayoyi.

The Guardian tace NDLEA ta bada sanarwar damke wani Usman Bokina Bajama wanda aka fi sai da Clemen a garin Mayo Belwa a jihar Adamawa.

Darektan yada labarai da wayar da kan al’umma na NDLEA, Femi Babafemi yake cewa a Talatar makon jiya wannan tsoho ya fado hannun hukumar.

Kara karanta wannan

Borno: Zulum Ya Sanar da Abun Mamakin da Ya Faru da 'Yan Ta'adda Wanda Ba a Taba ba a Duniya

Jami’an na NDLEA sun samu Usman Bokina Bajama dauke da kilogiram 49 da ya mallaka daga wata gonarsa da yake shuka taba a Mararraban Tola.

NDLEA ta kamo mutane 22

Babafemi ya kuma tabbatar da cewa wannan tsoho shi ne kan gaba a jerin mutane 22 da aka yi ram da su bisa zargin mu’amala da mugayen kwayoyi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda Kakakin hukumar ya fada, an yi nasarar karbe fiye da kwalabe miliyan daya (1,001,387) na Akuskura da aka haramta yin amfani da shi.

Hukumar NDLEA
NDLEA sun kama Usman Bokina Bajama Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Jaridar Tribune tace baya ga maganin Akuskura da kuma tramadol da aka samu, jami’an NDLEA sun karbe kilogiram 2, 536 na tabar wiwi a jihohi.

A jawabinsa, Babafemi yace an lalata eka goma na miyagun kwayoyi da aka shuka a gonaki. NDLEA tayi wannan aiki ne a garuruwan Edo da Adamawa.

Kara karanta wannan

Ana ji Ana Gani, Fasinjoji Sun Babbake Kurmus da Mota Tayi Hadari a Kusa da Gada

An kama dilalan Akuskura

A jihar Kwara, kwalaben Akuskura da aka karbe sun kai 19, 879. A nan ne aka kama wasu da ake zargi da laifi; Oladokun Oluwaseun da Ibrahim Jimoh.

Oluwaseun da Jimoh sun boye Akuskuran ne a cikin buhuna za a kai su garuruwan Ibadan da Jos a jihohin Oyo da Filato domin a saidawa Bayin Allah.

Haka zalika an kama Ukoro Ifeanyi da Idowu Toyosi a tashar Mararaba da ke Ilorin da kwayoyi 2, 290 na tramadol da kwalabe kimanin 100 na Codeine.

A garin Dansarai da ke Kano an kama masu saida kwayoyin, haka abin yake a hanyar Okene da kuma garuruwan Ovia da Uhunmonde a jihar Edo.

Buhari ya yabi Marwa

Kun ji labari Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jinjina na musamman ga shugaban hukumar NDLEA ta kasa, Buba Murwa kan irin kokarin da yake yi.

Kara karanta wannan

Ana Samun Rabuwar Kai a Kamfe Saboda Tinubu Ya Jawo Gwamna, Ya Ba Shi Mukami

Kamar yadda aka kawo rahoto, Buhari ya kira Buba Marwa daga kasar waje ta wayar salula domin yabon abin kwazon da jami’ansa suke yi dare da rana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel