Rashawa a Najeriya
Mai shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya tura tsohon dan majalisar Kaduna, Dabo gidan yarin Kuje har sai an yanke hukunci kan belinsa.
Gwamnatin Kano ta ce ba za ta sassauta wa duk wanda aka kama da laifin cin hanci da rashawa da rashin da'a a jihar ba. Mataimakin gwamna, Gwarzo ne ya fadi haka.
Arewa Consultative Forum (ACF) ta yi Allah-wadai da binciken da EFCC ta je tana yi a Dangote. Bello Sani Galadanci ya ce hakan ba zai jawo komai ba sai illa.
Hukumar EFCC ta gayyaci wasu manyan jami'an ma'aikatar jin kai a jiya Laraba, ta yi masu tambayoyi kan hannunsu a karkakatar da biliyoyin kudade daga ma'aikatar.
Yadda rikicin mata 2 yayi sanadiyyar tonon sililin ‘satar miliyoyi’ a gwamnati. Da alamar Halima Shehu ta taimaka wajen ganin bayan Betta Edu a kujerar Minista.
Ibrahim Shekarau ya ba Bola Tinubu shawara da ake ganin mai amfani ce. ‘Dan siyasar ya ce mukaman da shugaban kasar ya nada sun yi yawa idan ana son rage kashe kudi.
Shehu Sani ya yaba ma Shugaban kasa Bola Tinubu kan daukar matakin gaggawa a takkadamar ministar jin kai, Betta Edu, na badakalar kudi a ma’aikatarta.
Daga cikin manyan kudaden da hukumar EFCC za ta kashe a 2024 akwai naira biliyan 1,055,633 na tafiye-tafiye, da naira miliyan 413 na sayen motoci.
Hukumar NSIPA ta ce ministar jin kai da kawar da talauci, Betta Edu bata da hannu a kowani irin hada-hadar kudi ko zartar da hukunci a cikin hukumar.
Rashawa a Najeriya
Samu kari