Betta Edu: Rigimar da Ta Jawo Halima Shehu Ta Fallasa Minista Aka Yi Mutuwar Kasko

Betta Edu: Rigimar da Ta Jawo Halima Shehu Ta Fallasa Minista Aka Yi Mutuwar Kasko

  • Akwai alamun cewa Halima Shehu ta samu sabani da Betta Edu ne wanda ya jawowa dukkansu matsala
  • Bayan an dakatar da shugabar NSIPA, sai aka fara tono zargin laifuffuka a kan Ministar jin kai ta Najeriya
  • Babu mamaki Halima Shehu ta taimakawa wajen fallasa sirrin Edu wanda yanzu EFCC ta na bincike a kanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Akwai zargin rashin gaskiya iri-iri a ma’aikatar jin-kai da yaki da talauci, hakan ya shafi ministocin da aka yi a tarihi.

A farkon shekarar nan aka dakatar da Halima Shehu daga matsayinta na shugabar tsare-tsare na NSIPA, Legit ta kawo labarin.

Betta Edu
Betta Edu da Halima Shehu Hoto: @edu_betta/Liberty
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya canza shugaban NSIPA

Bayan nan sai aka nada Akindele Egbuwalo ya zama sabon shugaba a NSIPA ta kasa yayin da ake binciken satar kusan N40bn.

Kara karanta wannan

Badaƙala: EFCC ta tatsi muhimman bayanai, ta ɗauki mataki kan ministar da Tinubu ya dakatar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ba a dade ba sai aka ji labari ana zargin Betta Edu da laifin karkatar da N585m, laifin da ya jawo aka dakatar da ita ma daga aiki.

Hadimin Betta Edu ya kare Minista

Rasheed Zubair wanda hadimin ministar ne ya ce ana jifan Betta Edu da zargi ne saboda ta bankado barnar da ake yi a NSIPA.

The Cable ta kawo rahoton da ya yi bayanin yadda rigimar Edu da Halima Shehu ta fara.

Meya hada Halima Shehu da Betta Edu fada?

Kafin Bola Tinubu ya zabi Halima ta zama shugabar NSIPA, hadimar Betta Edu, Delu Yakubu aka fara yin tunani za a ba mukamin.

Wasu manyan jami’an gwamnatin tarayya da sanatoci sun nuna Delu Yakubu ba za ta iya wannan aiki ba, sai aka yi watsi da ita.

Majiyoyi sun ce Dr. Edu tayi niyyar aiki da Delu Yakubu ne, ta fi dadinta a kan Halima Shehu, tun daga nan aka fara samun sabani.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Shekarau ya yaba, ya fadi abin da ya ragewa Tinubu ya aikata a ofis

Kudi: Betta Edu v Halima Shehu

Na kusa da jami’an su na zargin lamarin kudi ya shiga tsakaninsu, ministar ta rika cire kudin NSIPA ba tare da shugabar ta sani ba.

Wannan abin ya fusata Halima Shehu, sai ta nemi ta dauke kudin da su ka rage a asusun hukumar domin tayi maganin ministar.

Domin takawa Edu burki, aka kawo Akanta Janar ta rika sa hannu a asusun NSIPA, kuma aka sanar da EFCC abin da yake faruwa.

Saura Tunji-Ojo bayan Betta Edu

Tsohon kamfanin Olubunmi Tunji-Ojo ne ya samu kwangila daga Betta Edu da aka dakatar, an ji labari hakan ya bar baya da kura

Ana so Bola Tinubu ya binciki Ministan cikin gida yadda EFCC ta ke bincike a kan Dr. Edu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel