Masu Garkuwa Da Mutane
'Yan bindiga dauke da miyagun makamai sun kai hari makarantar kwana, inda suka kashe mataimakin shugaba, suka sace dalibai masu yawan gaske a jihar Kebbi,
Rahotanni daga jihar Kwara sun nuna cewa yan bindiga sun yi garkuwa da Alhaji Abubakar Sise, dan kasuwa kuma tsohon shugaban PDP a mazabar Boriya–Shiya.
‘Yan bindiga sun tare fasinjoji a hanyar Ayere–Kabba, jihar Kogi, inda suka kashe mutum ɗaya, suka sace wasu, yayin da gwamnati ke cewa tsaro ya inganta da 81%.
‘Yan gida daya su 2 da aka sace a Imoga, jihar Edo, sun tsero bayan masu garkuwar su sun yi bacci a daji, yayin da aka nemi gwamnati ta kafa ofishin ‘yan sanda.
Yan bindiga sun kashe mutum 5, sun sace mata 9 a Bargaje, karamar hukumar Isa, jihar Sokoto. Yanzu haka dai yaran rikakken dan ta'adda Bello Turji, ne ake zargi.
Gwamnatin Kaduna ta ce ta ceto mutane 500 daga hannun ‘yan bindiga ba tare da biyan kudin fansa ko amfani da karfin makami ba. Kwamishina ya yi bayani.
Wani sautin murya da ake zargin na mataimakin kakakin Majalisar Kebbi, Hon. Sama'ila ne ya fara yawo, an ji yana neman a gaggauta hada kudin fansa.
Ƴan sanda a jihar Delta sun kama masu garkuwa uku, sun kwato N4.1m na kudin fansa da bindigar AK-47, sun kuma ceto wata mata da aka sace a Obinomba.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Edo sun samu nasarar cafke wata matar aure da ta shirya shirin yin garkuwa da ita don karbar kudade a hannun mijinta.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari