Masu Garkuwa Da Mutane
Bayan kwanaki 56 a hannun masu garkuwa, Janar Tsiga ya samu 'yanci. Iyalansa sun biya kuɗin fansa, amma an ci gaba da tsare shi na tsawon sati guda.
Wasu shugabannin 'yan bindiga a jihar Zamfara sun haukace bayan shan miyagun kwayoyi. Wasu na ganin zafafan addu'o'i da ake musu ne yasa suka haukace.
Dakarun Najeriya sun kashe Kachalla Dan Isuhu a jihar Zamfara. Dan Isuhu ya sa haraji a kauyuka 21, ya kashe Farfesa Yusuf na jami'ar Bayero, ya sace mutane da dama.
'Yan bindiga sun sace babban malamin addini, Rev. Fr. John Ubaechu a Imo. ’Yan sanda sun fara bincike, yayin da Kiristoci ke addu’a don kubutarsa.
‘Yan bindiga sun sace dalibai 2 a jami’ar FUDMA, da ke jihar Katsina yayin da aka ceto wani wanda aka yi garkuwa da shi a Adamawa, an kuma kama malami a Jigawa.
Bayan shafe fiye da wata daya a hannun yan bindiga, ana na ci gaba da riƙe Janar Maharazu Tsiga a da aka yi garkuwa da shi tun a farkon watan Fabrairun 2025.
Jami'an tsaro sun samu gawar sarkin da aka sace a birnin tarayya Abuja. An sace sarkin ne a gidansa a abuja tare da hadawa da wasu jikokinsa da wasu mutaneabuja
Jami’an tsaro sun dakile wani harin ‘yan bindiga a jihar Katsina, inda suka kashe dan ta'adda daya, sannan suka kwato makamai, babura da sauran kayan aikin miyagun.
'Yan bindiga sun kafa sansani a Bakori, inda suke kai hare-hare. An rahoto cewa suna kokarin mamaye Tafoki, Faskari, Funtua da Danja, inda jama'a ke tserewa.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari