Manyan Labarai A Yau
Tsohon mai tsaron gida na tawagar Super Eagles ta Najeriya, Vincent Enyeama, ya rasa mahaifinsa. Enyeama yanzu ya zama maraya bayan rasuwar mahaifiyarsa a baya.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Neja sun kai wani samame a wnai gidan gonar kiwon kaji da ke jihar. 'Yan sandan sun gano tarin alburusai a gidan gonar.
Atiku Abubakar ya yi magana a X, ya fadawa Bola Tinubu dole a rage facaka da dukiya kuma a yi gwanjon kadaroin Najeriya kamar yadda Javier Milei ya yi a Argentina.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mummunan gobara ta tashi a gidan karamar ministan birnin tarayya, Abuja, Dr Mariya Mahmood da ke unguwar Asokoro a yau Lahadi.
Kungiyar SERAP ta maka gwamnonin Najeriya tare da ministan babban birnin tarayya kara a gaban kotu kan kudaden da ake warewa kananan hukumomi a kasar nan.
Tsohon dan majalisar wakilai, Dr Usman Bugaje, ya bayyana cewa wasu shafaffu da mai ne na kusa da Shugaba Tinubu suka ba shi gurguwar shawara kan rikicin Nijar.
An kashe ‘yan bindiga da dama a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan bindiga da ke gaba da juna a kusa da Mada hanyar Gusau da karamar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo, Eze Madumere, ya rasa mahaifiyarsa, Ugoeze Marlinda Chikanele Ulunma a wani asibiti a lokacin da ta je duba lafiyarta.
Wata mai siyar da kayan gwanjo ta cika da mamaki bayan da ta tsinci dala 200 a cikin kayan gwanjon da ta siyo. Yan Najeriya sun yi martani sosai a kan hakan.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari