Tsohon Dan Wasan Super Eagles Ya Yi Babban Rashi a Rayuwarsa

Tsohon Dan Wasan Super Eagles Ya Yi Babban Rashi a Rayuwarsa

  • Tsohon mai tsaron gidan tawagar Super Eagles ta Najeriya, Vincent Enyeama, ya rasa mahaifinsa kuma kocinsa, Phillip Enyeama
  • Enyeama mai shekaru 41 ya sanar da rasuwar mahaifinsa ne ta shafinsa na Instagram a ranar Asabar, 24 ga watan Fabrairun 2024
  • Da yake jawabi, Enyeama ya ce yana alfahari da kasancewarsa ɗa a wajen mahaifinsa wanda ya taka rawar gani a rayuwarsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Tsohon golan Super Eagles, Vincent Enyeama, ya sanar da rasuwar mahaifinsa, Phillip Enyeama.

Ya bayyana hakan ne a wani saƙon ta'aziyya tare da wani faifan bidiyonsa tare da marigayin mahaifinsa suna wasan ƙwallon tebur a shafinsa na Instagram a ranar Asabar, 24 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnatin Tinubu ta shirya rabon tallafin N25,000 ga 'yan Najeriya

Mahaifin Vincent Enyeama ya rasu
Mahaifin Vincent Enyeama ya bar duniya Hoto: @vinpee
Asali: Twitter

Enyeama, duk da haka, bai bayar da cikakken bayani kan shekarun mahaifinsa da ya rasu ba, ko wurin mutuwarsa ko kuma sanadin mutuwarsa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Labarin mai ban tausayi ya mayar da tsohon mai tsaron ragar ta Super Eagles maraya bayan ya rasa mahaifiyarsa kimanin shekaru tara da suka gabata a shekarar 2015.

Marigayin, Phillip Enyeama ya taka rawar gani sosai wajen horar da ɗansa a farkon fara taka ledarsa.

Me Enyeama ya ce kan rasuwar mahaifinsa?

A cikin saƙon ta'aziyyar, ɗaya daga cikin fitattun masu tsaron gida a nahiyar Afirika ya rubuta cewa:

"Dukkan yabo ya tabbata ga Allah kan yin rayuwa mai kyau. Kai ne dalilin da ya sa mutane da yawa suka cimma nasarar da suka samu. Ka kasance marasa son kai da kyauta. Ka tsaya kan mutane da dama, ka jajirce domin mutane da dama su cimma burinsu. Ina alfaharin kasancewa ɗa a wajenka. Lokaci ne, na ka ya yi. Ina maka bankwana. Allah ya jiƙanka da rahama."

Kara karanta wannan

Jama'a sun daka wa tirelar kayan abinci wawa a jihar Katsina? An gano gaskiyar abinda ya faru

Vincent Enyeama ya buga wasanni 101 ga tawagar Super Eagles kafin ya yi ritaya daga buga wa Najeriya wasa.

Mahaifiyar Tsohon Mataimakin Gwamnan Imo Ta Rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa mahaifiyar tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo, Eze Madumere ta yi bankwana da duniya.

Marigayiya Ugoeze Marlinda Chikanele Ulunma Madumere, JP, ta riga mu gidan gaskiya tana da shekaru 83 a duniya.

Dattijuwar ta yi bankwana da duniya ne bayan ta je asibiti domin a duba lafiyarta kamar yadda ta saba yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel