An Maka Gwamnonin Najeriya da Wike Kara a Gaban Kotu Kan Abu 1

An Maka Gwamnonin Najeriya da Wike Kara a Gaban Kotu Kan Abu 1

  • Ƙungiyar SERAP ta shigar gwamnonin Najeriya da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ƙara a gaban kotu
  • SERAP ta shigar da ƙarar ne bisa zargin gazawar gwamnonin na bada cikakken bayani kan yadda aka yi da N40trn na ƙananan hukumomi
  • Ƙungiyar tana son kotun da ta tilasta gwamnonin da Wike yin bayani kan yadda aka yi da kuɗaden da gwamnatin tarayya ta ba ƙananan hukumomi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja – Ƙungiyar SERAP ta maka gwamnonin Najeriya da Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja ƙara a gaban kotu.

An gurfanar da gwamnonin da Wike a gaban kotu kan zargin gazawarsu wajen yin bayani kan ɓacewar Naira tiriliyan 40 da gwamnatin tarayya ta ware wa ƙananan hukumomi a jihohi da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnatin Tinubu ta shirya rabon tallafin N25,000 ga 'yan Najeriya

An kai gwamnonin Najeriya kara
SERAP ta shigar da gwamnoni kara a gaban kotu Hoto: @govwike
Asali: Facebook

SERAP ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 25 ga watan Fabrairun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙarar ta biyo bayan tonon sililin da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi wanda a watan Disamban 2022, inda ya bayyana cewa:

“Idan kuɗin da ake samu daga asusun tarayya zuwa na jiha ya kai kusan N100m, za a aika wa shugaban ƙaramar hukuma N50m amma zai sanya hannu akan cewa ya karɓi N100m. Daga nan sai ya sanya sauran a aljuhunsa.

Wacce buƙata SERAP ke nema a kotun?

SERAP ta shigar da ƙarar ne mai lamba FHC/ABJ/CS/231/2024 ranar Juma’ar da ta gabata a babban kotun tarayya da ke Abuja.

SERAP na neman kotun da ta umurci gwamnonin su wallafa cikakken bayani kan kason da ƙananan hukumomi suka samu daga gwamnatin tarayya da yadda aka kashe kuɗaɗen a jihohinsu tun daga shekarar 1999 har zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gamu da sabuwar matsala, ASUU zata sa kafar wando ɗaya da FG kan muhimmin abu 1

SERAP ta kuma roƙi kotun da ta tilastawa Wike ya wallafa cikakken bayani kan kason da gwamnatin tarayya ta ware wa ƙananan hukumomi a babban birnin tarayya Abuja da kuma yadda aka fitar da kuɗaɗen tun daga shekarar 1999 har zuwa yanzu.

SERAP Ta Kai Karar Akpabio da Abbas

A wani labarin kuma, kun ji cewa SERAP ta maka shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da kakakin majalisar Wakilai, Tajudden Abbas kan Naira biliyan 110 na motoci da tallafi.

Majalisun guda biyu za su kashe Naira biliyan 40 don siyan motocin alfarma guda 465 da kuma biliyan 70 na tallafi ga sabbin mambobin majalisun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel