Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Tsohon Mataimakin Gwamnan Imo Ya Yi Babban Rashi Na Mahaifiyarsa

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Tsohon Mataimakin Gwamnan Imo Ya Yi Babban Rashi Na Mahaifiyarsa

  • Mahaifiyar tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo, Eze Madumere, ta riga mu gidan gaskiya tana da shekaru 83 a duniya
  • Ugoeze Marlinda Chikanele Ulunma Madumere, JP, ta kwanta dama yayin da ta ziyarci asibiti domin duba lafiyarta kamar yadda ta saba
  • A wata sanarwa da gidan sarautar ya fitar, za a sanar da tsare-tsare da bayanai kan jana'izarta nan bada jimawa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Imo - Ugoeze Marlinda Chikanele Ulunma Madumere, JP, mahaifiyar tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo, Eze Madumere, ta riga mu gidan gaskiya tana da shekaru 83 a duniya.

Sakaraten masarautar Ezi-Mbieri, Cif Vincent Oparaji Agunechemba ne ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Lahadi, 25 ga watan Fabrairu, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Rayuka 7 sun salwanta saboda turmutsitsi a wajen siyan shinkafar kwastam a jihar APC

Mahaifiyar mataimakin gwamna Imo ta rasu
Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Tsohon Mataimakin Gwamnan Imo Ya Yi Babban Rashi Na Mahaifiyarsa Hoto: Prince Eze Madumere for Governor 2019
Asali: Facebook

A cewar sanarwar, dattijuwar ta amsa kiran mahaliccinta ne yayin da ta ziyarci asibiti domin duba lafiyarta kamar yadda ta saba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayiyar ita ce babba kuma kuma Ugoeze ta Mai martaba Eze Henry Anoruo Madumere JP, basaraken masarautar Ezi-Mbieri a karamar hukumar Mbaitoli.

Sanarwar na cewa:

"A 'yan kwanaki da suka gabata, a ziyarar da ta kai asibiti domin duba lafiyarta kamar yadda ta saba, lafiyarta ta kara tabarbarewa kuma bata tashi ba.
"Muna rokon ku cikin kankan da kai da ku tuna da ahlin sarki Madumere a cikin addu'o'inku don Allah ya ji kan mahaifiyarmu."

Sakataren masarautar ya kara da cewar za a sanar da tsare-tsare da karin bayani kan jana'izarta nan ba da jimawa ba.

Ku tuna cewa Madumere ya kasance tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo wanda 'yan majalisa suka tsige a ranar 30 ga watan Yulin 2018.

Kara karanta wannan

"Ban san me ya hau kaina ba": Matashi ya sheke mahaifiyarsa, ya kona gidansu

Rayuka 7 sun salwanta wajen siyan shinkafar kwastam

A wani labari na daban, mun ji cewa jam'iyyar APC ta tabbatar da mutuwar daga daga ciki mambobinta, Comfort Adebanjo, da wasu mutum shida a wajen siyan shinkafar da hukumar kwastam ke siyarwa don rage tsadar rayuwa a kasar.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, jam'iyyar mai mulki ta tabbatar da hakan ne a wani sakon ta'aziyya da ta saki a ranar Asabar, domin alhinin wadanda suka rasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel