Manyan Labarai A Yau
Daya daga cikin 'yan takarar zaben fidda gwanin gwamna na jam'oyyar APC a jihar Edo, Honorabul Dennis Idahosa ya dira a hedikwatar jam'iyyar ta kasa.
Rahoton BBC ya bayyana adadin kwanakin da Shugaba Tinubu ya yi a wajen Najeriya, idan aka kwatanta da na magabacinsai, Buhari a cikin watanni 9 na farko a mulki.
Wani mutum da ya ziyarci shagon siyar da adaidaita ya cika da mamaki bayan an sanar da shi cewa miliyan 2.6 ake siyar da shi a yanzu. Ya daura laifin kan dala.
Mai alfama Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya shawarci 'yan Najeriya da su rika yin addu'a ga shugabanni maimakon zagi ko cin mutunci.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun tafka sabhwar ta'asa a jihar Anambra. 'Yan bindigan a yayin harin sun halaka shugaban kauye a jihar.
Gwamnatin tarayya ta shirya fara bada tallafin N25,000 ga 'yan Najeriya duk wata domin rage radadin halin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da ake fama da su.
Wasu ma’aurata sun koka yayin da bakin da suka gayyata suka ki hallara. Ma’auratan sun kasha fiye da naira miliyan 43 kuma suna sa ran samun baki 88.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi magana kan matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a kasar nan. Ya fadi hanyar da za a magance ta.
Mambobin majalisar dokokin Zamfara sun tsige kakakin majalisar, Bilyaminu Moriki, saboda matsalar tsaro da ta addabi jihar sannan suka maye shi da Bashar Gummi.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari