Kwankwasiyya
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir el-Rufa'i a wani masallaci a Abuja. Haduwarsu ya kara karfafa rade radin sauya shekar Kwankwaso.
Tsagin NNPP ya zargi 'yan Kwankwasiyya da jawo ficewar Sanata Kawu Sumaila da wasu jiga jigan NNPP zuwa APC. Ya nemi a yi sulhu da Rabiu Kwankwaso.
Jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano, ta nuna rashin damuwarta kan sauya shekar da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, ya yi zuwa APC mai adawa a jihar.
Tsohon kakakin majalisar Kano, Kabiru Alhassan Rurum, wanda yanzu ke wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure a majalisar wakilai, ya sanar da ficewarsa daga NNPP zuwa APC.
Sanata Kawu Sumaila ya tabbatar da cewa ya ajiye NNPP, yayin da ya ƙi bayyana jam'iyyar da ya koma,duk da ana hasashen zai iya faɗawa jam'iyya mai mulki ta APC.
Babban jigo a jam'iyyar APC kuma darakta a hukumar raya kogunan Hadejia da Jama'are, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya caccaki Buba Galadima da Hakeem Baba-Ahmed.
Sakataren yada labaran NNPP na kasa, Ladipo Johnson ya bayyana cewa maganganun Ganduje a rabuwar kai a jam'iyya ba shi da wani amfanin a zo a gani.
Fitaccen mawakin Kwankwasiyya, Abuabakar Sani Dan Hausa ya koma NNPP a hannun Sanata Rabiu Kwankwaso bayan ya sauya sheka zuwa APC a hannun Barau Jibrin.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zama abin magana kan rade-radin da ake yi na cewa zai koma jam'iyyar APC mai mulki.
Kwankwasiyya
Samu kari