Katsina
Gwamnatin Katsina karkashin Gwamna Dikko Radda ta rufe makarantun firamare da sakandire a fadin jihar saboda dalilai na tsaro bayan farmakin da aka lai Neja.
'Yan bindiga sun sako wasu daga cikin mutanen da suka sace a jihar Katsina. An sako mutanen ne a shirin sulhu da ake yi da 'yan bindigan domin samun zaman lafiya.
Gwamnatin Katsina ta umarci Malam Yahaya Masussuka ya kare kansa gaban malamai. Ana zargin karatuttukan malami sun sabawa koyarwar addinin Musulunci.
A labarin nan, za a ji cewa jami'an tsaron jihar Katsina sun yi nasarar ram da wasu mutane guda hudu da suka tabbatar da cewa sun mika bayanan sirri ga 'yan ta'adda.
Babban hafsan sojojin saman Najeriya, Air Marshal Sunday Aneke, ya sha alwashin kwato dukkanin wuraren da ke hannun 'yan ta'adda. Ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba.
Gwamnan jihar Katsina ya nuna alhini kan rasuwar Alhaji Nuhu Yashe, Bebejin Katsina, yana kiran wannan babban rashi ga iyalansa, al’umma da masarautar Kusada.
Am gudanar da wata zanga-zanga a wasu kauyukan jihar Katsina kan matsalar rashin tsaro. Mutanen dai sun fita kan tituna ne bayan hare-haren 'yan bindiga.
Dakarun sojojin saman Najeriya sun kai hare-hare kan 'yan ta'adda a wasu jihohin Arewacin Najeriya. Sojojin sun yi nasarar hallaka 'yan ta'adda da dama a hare-haren.
Sanata Muntaru Dandutse ya mika sakon ta'aziyya bisa rasuwar limamin masallacim yan Izala da ke Funtua, Sheikh Goni Imam Sa'id Musa, ya yi addu'ar Allah jikansa.
Katsina
Samu kari