'Yan Sanda Sun Ceto Mutanen da Aka Yi Garkuwa da Su a Katsina

'Yan Sanda Sun Ceto Mutanen da Aka Yi Garkuwa da Su a Katsina

  • Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Katsina sun samu nasarar kuɓutar da wasu bayin Allah da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su
  • Ƴan sandan sun ceto mutanen ne a dajin Kankara bayan an yi garkuwa da su a kanhanyarsu ta zuwa jihar Zamfara daga birnin tarayya Abuja
  • Kakakin rundunar wanda ya tabbatar da ceto mutanen ya ce miyagun da suka yi garkuwa da su za su shiga hannu nan bada jimawa ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Ƴan sanda a jihar Katsina sun ceto wasu mutum biyar da ake zargin an yi garkuwa da su ne a hanyar Abuja zuwa Zamfara.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu, ya tabbatar da ceto mutanen yayin da yake zantawa da manema labarai, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Bauchi: Adadin mutanen da suka mutu a wurin rabon zakkah ya ƙaru, an faɗi sunayensu

'Yan sanda sun ceto mutum 5 a Katsina
'Yan sanda sun ceto mutanen da aka sace a Katsina Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Kakakin ya bayyana hakan ne a Katsina a ranar Talata, 26 ga watan Maris 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'in ya ce tawagar ƴan sanda da ke aikin sintiri sun ceto mutanen ne a ranar Litinin daga dajin ƙaramar hukumar Kankara a jihar Katsina, inda aka ɗaure su da sarƙa, rahoton da jaridar Daily Post ya tabbatar.

A ina ƴan sanda suka ceto mutanen?

A kalamansa:

"Mutanen da aka kuɓutar sun fito ne daga Abuja zuwa Zamfara a ranar, 9 ga watan Maris lokacin da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Kushere da ke Zamfara.
"Bayan an yi garkuwa da su an kai su zuwa dajin Katsina inda aka ɗaure su, amma daga ƙarshe jami’anmu sun ceto su."

Ya ƙara da cewa waɗanda aka ceton na samun kulawa a asibiti domin duba lafiyarsu yayin da ake ƙoƙarin haɗa su da iyalansu.

Kara karanta wannan

Filato: An shiga tashin hankali bayan sabon rikici ya barke, bayanai sun fito

Sadiq-Aliyu ya bada tabbacin cewa ƴan bindigan da suka aikata wannan ɗanyen aikin za a cafke su.

Ƴan bindiga sun sace mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai farmaki a Kurechin Giye da ke yankin Makera a ƙaramar hukumar Dutsinma a jihar Katsina.

A yayin farmakin sun yi awon gaba da matan aure 12 tare da kwashe dukiyoyi na miliyoyin Naira na mazauna garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel